Thursday, December 17, 2020

FA_IDAR_AUREN_MIJI_MAI_GEMU

 


#FA_IDAR_AUREN_MIJI_MAI_GEMU.

πŸ’•πŸ’žπŸ’žπŸ’•πŸ˜„'YAN UWANA MATA KUZO KUJI WANI SIRRIπŸ˜πŸ˜„πŸ˜„πŸ’“πŸ’•πŸ’ž

Na Daga Cikin Fa'idar Auran Miji Me Gemu..
..
..
'Yar uwatah Matso kusa Domin kiji Sirrukan..πŸ₯°πŸ€©πŸ™ˆ

🀩1πŸ’ž Idan Allah ya Azurta ki da Miji Mai Gemu 'Yar uwatah kitayashi Gyaran sa..
Never Allow him Go out with Gemu Botsaa 🀨🀨🀨 Kamar Hammatan 'Yan Air..

Dazaran kin Gama shiryashi zai Fita ..
Ɗauko Kum taje mai Gemu Hajiya ta ..
Shafa mishi man Gemu inbabu
Samu mai me Ζ™amshi shafa mai..πŸ˜„πŸ˜„

'Yar uwatah kema dakanki xakiga Maigidan naki Ya chanja ..
Yayi kyau... Ya zama Ɗan kwalisaπŸ˜„πŸ€©

πŸ’ž2- 😍 Daga cikin Fa'idar Gemu...
Gemu da saje Suna Ζ™ara Ɗankon soyayya atsakanin Ma'auratah🀩😍
...

'Yar uwatah idan kuna zaune kuna fira keda maigida Never Allow that sitting yatafi a banza...
😍'Yar uwatah jawo fuskarsa ..
Dinga shafa Gemun nan ..
Kina Ι—an jan Gemun nan cikin salo da iya soyayyar...😍😍😍
Wallahi 'Yar uwatah xakiga Yana Ι—an lumshee Idanuwa...
Ma'ana yana jin daΙ—i
....Dinga bashi labarai masu daΙ—i..
Ce masa mijinah 😍 kasan ina sonka ko..
Lallai akullum jinake soyayyar ka Ζ™ara Girma take acikin zuciya tah...
Baa na tunanin akwai MACEN datakai Ni sa'ar miji a wannan DuniyarπŸ˜πŸ’žπŸ’•πŸ˜

Pls! 'Yan Uwana mukula sosai Dukkanin Abinda zai faranta ran mazajenmu idan muka Aikata lada zamu samu...
Wanda free ticket ne zuwa Aljannah
... Allah yadatar damuπŸ™πŸ€©πŸ˜

πŸ’ž3-😍 Na daga cikin Fa'idan Gemu ...
πŸ˜πŸ˜„πŸ˜„
Zaki iya hukunta mai gida dashi idan yamiki laifi....
Batare da Yasani baπŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„
πŸ™ˆπŸ™ˆπŸ™ˆπŸ™ˆ
Lokacin dakuke zaune musamman idan Yana cikin nishaΙ—i...
Samu Gemun nan kina shafa shi...
Ahankali .. xakiga Yana lumshe Idanuwa...
Daganan Kija gashin Gemun Da karfi .. sai ki maza kisaki...

Xakiga yayi fir-gi-git yana xari Idanuwa😳😳
Kamar wanda yayi Qarya...
Sabda Azabar zafi..πŸ˜„πŸ˜„πŸ€ͺπŸ€ͺ
Kekuma adai dai wanan lokacin ki sakar Masa Qayataccen Murmushi ..,Ki kashe masa ido Ɗaya😘

Shima zai mayar miki da martani murmushinki😍😊

Koba komai zuciyar ki tayi sanyi...😍😊🀩
Sai ku sa-santa kanku
....
MATA DA MIJI SAI ALLAH🀩😍😘

#Shawara_Ga_Maza..
HaΖ™iΖ™a barin Gemu SUNNAH ce babba ta Annabin Rahama S.A.W

Kaji tsoron Allah ka daina aske Gemu..
Wai don Kar Ace ka tsufa...
Kasani Gemu wata irin Qarin Girma ne da Darajar da cikar Haiba.. agareka
...

Jin jina Ga wasu daga cikin matasan mu..
Domin Yanzu sun fara ajee Gemuu..

Tabbas A wannan zamanin mata dayawa suna kwadayin Auren miji mai Gemu...
Mutumin kirki...

Adaure A dinga aje Gemuu..

Mata da Maza Allah nake Roko Ya zaΙ“a muku Abokanan zama Nagari. Yaa HAYYU Yaa QAYYUM 🀲

Na barku lafiyaπŸ™
..
Safeeyyah Suleiman Umar
GODIYA Agareka MijinahπŸ’•πŸ’žπŸ’•
Na bani dama da kayi...
Wajen Wayar wa 'Yan Uwana mata dakai..
Da sauran Al'ummar Musulmi..
Game da Zamantakewar yau da kullum..
Allah yasaka maka da Alkhairi..
16-Dec.2020

Tuesday, November 10, 2020

ADDUA GA YARAN MU

 


ADDUA GA YARAN MU
(1) Allah kayi min albarka a cikin 'ya'yana
(2) Allah kayi masu muwafaka su zamo masu yi maka biyayya
(3) Allah ka azurtani da suyi min biyayya
(4)Ya Allah yadda ka sanar da Annabi Musa ilimi ka sanar da 'ya'yana ilimi.
(5) Ya Allah yadda Ka fahimtar da Annabi Sulaiman Ka fahimtar da 'ya'yana.
(6) Ya wanda Ya ba Annabi lukman hikima. Allah ka Bawa Yaya na hikima kuma ka basu iya zance.
(7) Allah Ka bawa 'ya'yana ilimin da basu sani ba.
(8)Allah Ka tunatar da su abinda duk suka manta
(9) Allah ka budewa 'ya'yana albarkar sammai da kasa
(10) Allah Kai mai ji ne kuma mai amsawa ne.
(11) Allah ina rokonka, ka bawa 'ya'yana gam da katar .
(12) Ya Allah Ka basu karfin hadda, kuma Ka basu saurin ganewa,Ka basu kaifin tunani
(13) Allah kasa 'ya'ya na su zamo shiryayyayu, masu shiryarwa
(15) Allah Kai mai ji ne kuma mai amsawa
(16) Allah kar Ka sauyar da Imani a cikin zukatan su.
(17) Allah Ka kawata zukatansu da Imani, Ka sa masu kyamar kafircine
(18) Allah Ka sa masu kyamar fasikanci da kyamar sabon Ka ne
(19) Allah Ka sanya su cikin shiryayyayu.
(20) Allah ka gyara halayen 'ya'yana, Ka cika zukatan su da haske da hikima.
(21) Allah ka tsarkake zukatan 'ya'ya na ga barin riya.
(22) Allah Ka tsare mani gaban 'ya'yana, Ka kare su ga yin zina,Ka kare su daga yin luwadi,Ka kare su daga yin madigo ka kare su da dukkan
laifuffuka ka kare mani zuri'a ta.
(23) Allah Ka sanya 'ya'yana su zamo mahaddatan Al-Qur'ani,su zamo masana Sunnar Annabin Ka(SAW)
(24) Allah Ka azurta 'ya'yana da kamewa da yarda da hukuncin da kayi akan su
(25) Ya Allah Ka azurta 'ya'yana da kaunar Ka da kaunar Annabin Ka da kaunar duk wanda Kake kauna da kaunar duk wani aiki da zai kusantar dasu zuwa ga samun soyayyar Ka.
(26) Ya Allah Ka budewa 'ya'yana kofar arziki na halal daga mayalwaciyar falalar Ka kuma Ka wadatar da su da halal da barin haram.
(27) Allah ka nisantar dasu daga abokai ko kawaye munana da zasu bata tarbiyyar su ko halayen su Ka raba su da alfasha da dukkan mummunan abu.
(28) Allah kasa 'ya'yana su zama masu lafiya a jikin su, Ka kare masu kunnuwan su,Ka kare masu idanuwan su,Ka kare masu rayukan su,Ka kare masu gabbansu ga barin sabon ka ya mai jin kan masu jin kai .Amin Ya Rabbil Alamin.
DON ALLAH WANDA DUK YA SAMI WANNAN ADDUA TO YA TURAWA DAN UWA KO MU RIKA YIWA YARAN MU su zamo nagari.KUMA YA ZAMO SADAQATUL
JARIYA A GAREMU.ALLAH YA SHIRYA MANA SU KUMA YA ALBARKACI RAYUWAR SU AMIN

 

AKWAI DARASI A WANNAN LABARIN!!

 


AKWAI DARASI A WANNAN LABARIN!!
Akwai wani mahaukaci yana bara duk
abinda ka bashi sadaka sai yace
"kayuwa kanka°ranar wata kasuwa ya
shiga kasuwar domin bara,Ashe
akwai wata Mata tanajin haushin
wannan Kalmar da yake fada" wata
Rana ya dawo bara cikin
kasuwar,matar nan ta kirashi ta bashi
sadakar abinci Ashe ta saka guba
(poison) yana karba yace"kinyiwa
kanki• ya juya yayi tafiyarsa,kawai
Mata ta kwashe da dariya tace daka
yau bazaka sake cewa wani yayiwa
kansa ba
...yaje inda yake zama domin cin
abinda ya samo daka bara.kawai
saiga wasu yara sun taso daka
makaranta..sukace da
mahaukaci..kayiwa kanka yau meka
samo ne ka bamu bamu,yace ba
komai sai wani abinci gashi kuci.
suka karba suna murna yace dasu
idan kun gama Ku Kai kwanan cikin
kasuwa..aikuwa suna gamawa daya
Daga cikinsu yace wannan kwanan
kamar Na mamanmu,sukace ehh
shine°ai kuwa suka nufi kasuwa uwar
Na ganinsu da kwano tace a Ina kuka
samu kwano,sukace Kinyiwa kanki ne
ya bamu abinci mukaci
kawai uwar ta Fara kuka
Lallai nayiwa kaina°°'yan uwar mu
tuna duk abinda za muyi mai kyau da
Mara kyau kanmu mukeyiwa...domin
haka idan ka turawa ma wani wannan
sako kaima kayiwa kanka,nidai Na
tura muku Na yiwakaina.
Allah bamu ikon yiwa kanmu alheri.

 

MAI WA'AZI

 


MAI WA'AZI 
so tari in da zai tsaya ya kalli kansa ya duba ayyukansa,kansa ya kamata ya fara yiwa wa'azi kafin waninsa. Domin a Ɗabi'ah mai wa'azi wani lokaci ya kan manta da kansa,in ba wanda Allah yakiyaye shi ba.
Allah nake Roko Ya Ƙara Tabbatar da zuciyoyin mu akan Imani.🀲

IYA ZAMA DA MIJI


 

IYA ZAMA DA MIJI DAGA BAKIN MARIGAYI SHEIKH JA'AFAR (R).
.....................................✍🏼
1- Aurenki ya zama domin neman yardar ALLAh kikayi ba dan tara abin duniya ba.
2- Kada ki zama mai kwadayi wajen zaben mijin Aure.
3- Ki zabawa 'ya 'yanki uba ta hanyar Auren wanda ki ka yarda da addininsa da dabi'unsa harma da dangantakarsa.
4- Ki zama mai riko da addini a gidan mijinki.
5- kada ki zama mai kauracewa shimfidar mijinki.
6- Ki zama mai hakuri da halayyar mijinki.
7- Ki zama mai matukar biyayya ga mijinki.
8- Ki zama kwararriya wajen iya kwalliya kala-kala.
9- Ki zama kwararriya wajen iya girki kala-kala.
10- Ki zama kin iya barkwancin magana wajen baiwa mijinki dariya.
11- Kada ki zama mai rainuwa a cikin duk abinda mijinki ya baki.
12- Ki dinga wanke bakinki da safe da yamma da kuma lokacin kwanciya barci.
13- ki zama mai tsaftar jikinki, gidanki, abincinki, da sauransu.
14- Ki dinga girmama Iyayan mijinki da 'yan uwansa da abokansa.
15- Kada ki zama mai satar kayan mijinki.
16- Kada ki zama mai satar fita unguwa.
17- Ki guji Leke a gidan mijinki, dan yana daga cikin abinda yake raba Aure a tsakanin Hausawa.
18- Ki dinga godewa mijinki a cikin abinda ya baki.
19- ki kiyaye abinda mijinki ya fi so.
20- ki kiyaye abinda mijinki ya fi sonci da safe, rana, dakuma dare.
21- Ki dinga yabawa mijinki kwalliyarsa.
22- Ki dinga yawan neman shawarar mijinki akan duk wani al'amari da zaki yi.
23- Kiyi kwalliya ki tsane tsaf kafin dawowar mijinki.
24- Ki dinga sanya turaren wuta a dakinki, kuma ki kasance mai sanya turare a jikinki a duk lokacin kwanciya.
25- Lallai ki yi kokarin gama aikace-aikacenki kafin dawowar mijinki.
26- Kada ki bari mijinki ya dawo ya sameki gaja-gaja, ki sani kazanta tana haifar da kiyayya.
27- Ki zama mai yawan canza zanen kunshin kafarki da kuma zanen kitso.
28- Kada ki ce mijinki sai ya saya miki abinda ba shida ikon saye.
29- Lallai ki yi amfani da ilimi wajen yanke dukkan wani hukunci.
30- Ki yi shiru a duk lokacin da mijinki yake yi miki fada ko Nasiha.
31- Kada ki zama Al-mubazzara mara tattali.
32- Kada ki tara kayan wanki da yawa a daki, naki ko na mijinki suna wari.
33- Ki tanadi kayan kwalliyar gida bayan na zuwa unguwa.
34- Ki kula da yanayin da zai nuna miki cewa mijinki yana cikin Nishadi ko Damuwa.
35- Kada ki ringa baiwa kawayanki labarin sirrin dake tsakaninki da mijinki.
36- Idan zaki yiwa mijinki magana kiyi masa da tattaunsan harshe, da murya mai karya zukata.
37- Ki zama kin iya kallo mai nuna alamun sha'awa ko soyayya.
38- Idan kika samu sabani da mijinki ki bashi hakuri ko da kuwa kece da gaskiya.
39- Ki zama mai tattali a cikin dukkan abinda kika mallaka a gidan mijinki.
40- Kada ki zama mai kwauron baiwa dangin mijinki abinda ya umarceki da a basu.
41- Kada ki zama mai yin dare wajan girki.
42- Kada ki zama uwar adashi ba tare da sanin mijinki ba.
43- kada ki zama mai yawan fada da makwabtanki.
44- Kada ki kasance mai yawan zagi ko Ashariya.
45- Kada ki ringa baiwa Iyayanki Labarin laifin da mijinki yake miki.
46- Ki zama mai hakuri da juriya da halayyar Iyayan mijinki da 'yan uwansa.
47- Idan mijinki ya yi miki laifi kada ki nuna masa bacin ranki a gaban iyayanki ko 'yan uwansa.
48- Kada ki ringa daga murya sama idan kuna sa-in-sa da mijinki.
49- Kada ki rinqa baiwa 'yan uwan mijinki labarin laifukansa.
50- Ki dinga yiwa mahafiyar mijinki Ihsani da 'yanuwansa.
51- kidinga yiwa mijinki addua tamusamman kamar lokacin walha ko bayan yafita zuwa wajen nemo abinda zakuci kuyi sutura.
52- kizama mai son ibada, nesa nesa da qawaye da son zuwa neman ilimi na Addininki don Sanin yadda zaki bautawa Ubangijinki dasauransu, kuma ki nemi ilimin zamani don sanin yadda zaki zaman duniya cikin rufin asiri da sanin yakamata.
*Ga Amana nan mun baki/ka katurawa mata ko maza domin a Isar zuwa ga 'yan uwa mata kuma uwayenmu don ceto su damu gaba daya daga kaidi da tarkon shitan la'ananne.*
*Mugudu tare mutsira tare*πŸ‘

Thursday, October 29, 2020

SUNNAH LEKA GIDAN KOWA

 


NAZIYARCI BABBAN MASALLACHIN AUCHI

Yaa Allah ka Ζ™ara Daukaka SUNNAH ..
Allah ka Tsare mana 'Yan agajin mu,Da Maluman mu Na SUNNAH.🀲

JIYA Na halarci Wani Babban Masallacin juma'a a garin Ekabigbo AUCHI, (Edo State)
Abun Ya burgeni Yanda Na ga Yara mata da. ,'yan mata da kuma tsofaffi Mata sun cika Masallaci Domin Sallatar Juma'a. Abun Ya burgeni Wallahi...

Gefe kuma Ga SOJOJIN SUNNAH JIBWIS , wato 'Yan Agaji Mata da Maza ..

Alhamdulillah πŸ™
Duk da Kasancewar su Garine da 'Yan Bidi'a suka Yawaita, Amma hakan bai hana wasu Halartar wajen Ibada ba...

YAA! ALLAH KA ƘARA CUSA MUSU SON SUNNAH ACIKIN ZUKATANSU...

YA RABBI KA ƊAUKI RAYUKAN MU MUNA MUSULMAI AHLUSSUNNAH..
ALLAH KA AMSHI IBADUN MU..

ALLAH KA SAKAWA IYAYEN MU DA ALKHAIRI..
ALLAH ƘARA MUSU LAFIYA DA RAYUWA MAI ALBARKA...
ALLAH KAYI MUSU SAKA-MAKO DA GIDAN ALJANNAH..

WAƊANDA SUKA RASU ALLAH KA HASKAKA MUSU MAKWANCINASU ,ALLAH KASANYA ALJANNAH FIRDAUS TA ZAMA MAKOMA AGARESU..🀲

AMEEN YA HAYYU YAA QAYYUM.πŸ‘

Safeeyyah Suleiman Umar
24-Oct.2020

BA MUTUWARCE ABAR TASHIN HANKALI BA

 


Bafa Mutuwar bace Abar firgice da tashin hankali...

Abunda bawa zai tarar..
Idan yasamu akasin abinda yake tsammani zai riska,bai Samu ba .., Sai YafaΙ—a a mummunar Makoma..

Wannan shine Babban Tashin hankali..
Ya Allah ka cire mana Riya acikin Zukatan Mu..
Allah ka tsarkake mana niyyar mu...

Ya Rabb kasanYa dukkanin Abinda zamu Aikata shi,Mu Aikata shi Domin ka Ya Allah..
Allah ka hanamu Aikata Ayyuka Don Ayabemu ko ace Mun iya...

Allah kasa Mudinga Aikata Ayyukan mu Domin ka...
YAa HAYYU Yaa QAYYUM 🀲

Safeeyyah Suleiman Umar
17-Oct-2020

NAGARTA A ZAMANTAKEWA

 


NAGARTA A ZAMANTAKEWA

Tambaya:AssalamualaikiMalama a taimaka mana da yadda za a gyara amarya, na hadin gyara:

Amarya budurwa ce kuma bata da jiki sannan farace ?

Amsa: Wa.alaikumussalam, Da yake fara ce, kuma bata da jiki, sannan budura ce;

Tana bukatarfara gabatar da shan magungunan sanyi, kamar:

Yajin gora
Busassar tafarnuwa
Cittar zabibi
'Yayan zogale
Lawashin albasa
Jan karib

A hada su a busar, a gyara a nika sosai suyi laushi ta rika shan cokalin garin maganin da kunun aya koh kindirmo:

Sauran a nemi mazubi mai rufewa kam a zuba. Sannan a fara gabatar da wannan maganin da an tsaida ranar aure idan dai ba lokaci a ka sanya mai nisa ba.

Domin akasarin 'yan mata suna karatun boko, wanda ke tilasta amfani da bandaki mai kazanta, amfani da audigar mata, koh amfani da bandakin gidan taro:

Sannan 'yan matan mu na zamani baka shaidar su, gwanda a gyara su, domin kada su tafi su dawo.

πŸ‘ŒπŸΌKe uwa, ke ce dai da ya kamata ki lurar da ita ladabi a wurin miji, da rashin gaddama ga umarnin sa, yi nayi bari na bari, sannan ta kula da tsabta, gyara kwalliya, da sarrafa girki mai dadi mai kuma kyau da kudi 'yan kadan, wanda suna daga cikin sirrikan auratayya.

-------------------------------------
πŸ•‹Nisa'us Sunna

Copied

 

GWALA-GWALAN MALLAKAR ZUCIYAR MAIGIDA

 

 


GWALA-GWALAN MALLAKAR ZUCIYAR MAIGIDA

TSABTA DA KWALLIYA

Lallai kowani Namiji yana son matarsa ta kasance a koda yaushe cikin tsabta da kwalliya, ta yadda ba zai ga wasu matan a waje ba sunyi kwalliya su burge shi ba, amma a yau mun wayi gari da yawa daga cikin Mata suna yin sakaci da tsabta da kwalliya ta yadda matan waje masu iya kwalliya da ado da tsabta su ke janye zuciyar mazajensu.

Saboda haka 'Yar uwa ki tunani kuma ki sani ke ba mummuna ba ce, ki tashi tsaye ki zama koda yaushe cikin tsabta da kwalliya. Ki kasance ga mijinki tamkar kyakkyawar fulawa mai furanni iri-iri na kyau tare da shekin iska mai kamshi a tare dake da kuma kyakkyawar shiga ta kaya irin mai jan hankalin miji.

GWALA-GWALAN MALLAKAR ZUCIYAR MAIGIDA

IYA RARRASHIN MIJI

Tabbas rayuwar aure rayuwace ta haΖ™uri, dole wata rana za a samu saΙ“ani. Shi dai rarrashi abu ne da mazaje suke jin daΙ—insa a zukatansu, musamman kuma ace mace ta san hanyoyi daban-daban na tarairayar miji.
Macer da ta iya rarrashin miji ita ce wacce in ta vatawa mijinta rai kuma ta ga alamun haka a fuskarsa, takan je kusa da shi ta zauna ta bashi hakuri ta hanyar amfani da wasu kalmomi masu taushi masu tsada.

Shiyasa Nana Khadijah {r.a} ta yiwa matan Duniya fincinkau wajen iya rarrashin miji kamar yadda ya tabbata a tarihi. A lokacin da Manzon Allah {s.a.w} ya dawo daga Kogo cikin firgici, amma saboda kwarewarta wajen iya rarrashin miji sai ta nuna masa cewa ai babu abin da zai sameshi in sha Allah domin yana sada zumunta da sauransu.

Abin tambayata anan shin matan yanzu in su ka Ι“atawa mazajensu rai ko suka dawo cikin bacin rai haka suke musu?

Copied/Dan uwanku a Musulunci: Yusuf Lawal Yusuf

GWALA-GWALAN MALLAKAR ZUCIYAR MAIGIDA

KISHIN MIJI

Sannunku da aiki ya ku mabiya wannan rubutu nawa, a yau zan ci gaba da lissafo muku wadannan gwala-gwalan da nike bayani a kansu. Hanya ta gaba da Mace za tabi domin mallake zuciyar maigida shine: KISHIN MIJI. Duk Mace ta gari tana kishin mijinta, ita ko kalmar "KISHI" kamar yadda Sheikh Basheer Lawal Muhammad Zaria ya anbata a wani rubutu nasa ya ce: kalma ce mai wuyar fassarawa amma za mu iya cewa: Kishi wani abu ne a zuciya da ke sa a damu matuΖ™a da abin da ake so, kuma a Ζ™i alfarmar wannan abu ta zube, kuma ake kaffa-kaffa da shi, da gudun kar wani ya rabauta da shi fiye da shi mai sonsa.

Saboda haka, ya ke Ζ΄ar uwa ki zama mai kishin mijinki a ko ina yake, ta hanyar nuna damuwarki lokacin da kika ga ya shiga wani hali, idan bai da lafiya kiji kamar kece baki da lafiya idan zai fita aiki ki rakashi, idan ya isa wajen aikin ki kirashi bayan ya dauki wayar sai kice: Jarumina, ko Hasken idanuna, ko baban wane ina fatan ka isa lafiya?.

ƁOYE ABIN SONKI SHINE KISHINSA, KISHINSA KUMA ALAMAR SONSA NE.

Zamu dakata anan sai mun hadu a rubutu na gaba in sha'allah.

Copied Yusuf Lawal Yusuf

 

 

MAFARKINAH JIYA DA DADDARE

 




 ( MAFARKINAH JIYA DA DADDARE)πŸ’ž
Ku biyoni kusha Labari
πŸ’žπŸ’“πŸ’ž

Annabi S.A.W Ya-ce " Mafarki Mai kyau daga Allah ne..
...Mafarki Mara kyau daga shaiΙ—an ne..

Malamai sunyi Ζ™arin bayani Game da mafarki Mai kyau .. zaka iya bayyanawa..
Mafarki mara kyau kuma idan kayi ka nemi tsari daga shaiΙ—an kayi tofi sau uku.. kuma mutum ya ka-me bakinsa basai ya bayyana ba..

Alhamdulillah πŸ™πŸ˜
Sabda Wannan Dalilin ne ,nakeso bayyana mafarkin danayi daren jiya.
.
Tare da wata baiwar Allah,wacce friend dita ce.. tsawon shekaru da dama a wannan kafa ta Sa-da zumunta...
Ban taΙ“a ganinta ido-da ido ba,..

WALLAHI BAN SANTA DA WANI AIKI BA, FA-CE AYYUKAN ALKHAIRI A WANNAN KAFA TA FACEBOOK SOSAI,WAJEN DA'AWA ,FAƊAKARWA ..
ALLAH YASAKA MATA DA ALKHAIRI.

Allah cikin ikon sa,Ƙudirar sa.., jiya nayi Mafarki da ita Malama Faridah Bintu Salis ,😍

Na Gammu acikin wani babban masallaci.., Masallacin yayi kama da masallacin juma'a, Muntara Mata dayawa Bila adadin .., masallacin yacika MaQil da Mata..

Mu kuma muna kan wasu kujeru a saman step.. ko wacce da Alarammiyyar ta, Nafara tafsirin Alkur'ani Mai Girma acikin سورة عبس
🎀🎀🎀

Alarammiyya ta wacce bansan ko wacece ba a mafarkin tana jaa min BaQee Ni kuma ina FASSARAWA... Idan nayi nagaji sai Malama #Faridah_Bintu_Salis ta Ζ™arΙ“a taci gaba da tafsirin Ana jaa mata baQee ..🎀🎀
Mata na sauraren tafseerin Alkur'ani mai Girma daga bakunan mu..🎀🎀🎀

Agefe kuma wani Malamin Islamiyyar mu ne a Zamfara..
Malam Muhammad Sani Abdulkarim Gusau.
Shugaban makarantar Ω…Ψ―Ψ±Ψ³Ψ© Ψͺربية Ψ§Ω„Ψ₯Ψ³Ω„Ψ§Ω… ΨͺΨ―ΩˆΩ† ودا غسو.

Shiyake Guiding din mu idan wata kalma ,fassarar ta tashige mana yafassara mana..

Ana cikin haka Ina tafseerin sai wasu kalmomi suka shige mun , namanta fassarar su..
Kalmar ΨΉΨ¨Ψ―
(Abdu)

Da kuma ΨΉΨ±Ψ¨Ψ§
(Urbaa)

Sai na tambayi Malama #Faridah fassarar su sai tace wallahi Malama nima fassara ta shige mun...

Sai na tambayi wannan malamin namu na Islamiyyah ,Sai Ya tuna mana fassarar kalmomin ,muka ci gaba da tafseerin Abun mu..
😍
Anan Nafarka da Dadda Ι—an Mafarkinah na daren jiya..
Around 2:10am Na dare...
Wallahi sabda farin ciki nakasa komawa barci,ina ta tasbihi ga Allah, Na dauki tsawon lokaci kafin wani baccin Ya daukeni..

Alhamdulillah πŸ™
Allah nake Roko Ya tabbatar da wannan Mafarkin nawa..

Annabi S.A.W Yace"Mafi Alkhairin ku,Wanda Ya koyi ALKUR'ANI KUMA YA KOYAR DASHI."

Yaa! Ka bamu ilimin wannan littafin naka,
Mu amfanar da Al'umma dashi..
YAa HAYYU Yaa QAYYUM.

Dukkanin wani ko wata da Take da babban Buri akan Littafin ka Mai Tsarki..
Allah ka sauΖ™aΖ™e mana hanyar koyon shi ,Muhaddaceshi,Mu amfanar da Al'umma dashi..

YAa HAYYU Yaa QAYYUM 🀲
Allah kasanYa AlΖ™ur'ani yacecemu Ranar Gobe kiyama.

Ina miki Fatan Alkhairi.
Malama #Farida_Bintu_Salis

Safeeyyah Suleiman Umar
25-Oct.2020.

SHEIK ALBANY (RAHIMAHULLAH)


 

Sunana Muhammad Auwal
Sunan Mahaifina Adam
Sunan mahifiyata Saudah
Abu - Abdirrahman shine Alkunyana
Albaniy shine Lakabina
An haifeni a Anguwan Muciya Sabon Garin
Zaria a shekarar 1960
Nayi makarantar Allo har nayi sauka
Na koyi littafan da akeyi a zaure na fiqhu
dana lugah da Adab
Nayi karatu a wurin manyan malamai
mabanbanta a kasata Najeriya da kasashen
waje inda na koyi Qur'ani da dukkan
kira'o'insa, Hadisi da musdalah dinsa, Tafsiri
da Usul dinsa, Tareekh da usul dinsa,
Aqeedah da Manhaj da usul dinsu, Harshen
larabci da fannoninsa, Fiqh da Usul da
Qawa'id dinsa, d.s
Nayi makarantar firamare a Sabon Garin
Zaria
Nayi Sakandire a kwalejin Barewa Zaria
Nayi Diploma akan:
Law
Computer Science
Mass Communication
Hausa Language
Nayi Degree akan ICT
Nayi Masters akan Islamic Studies
Ni Professional Jounalist ne
Ni Certified Microsoft Engineer ne
Ni Linguistic ne
Na karanci Library Science
Nayi Programme na N+ akan Computer
Nayi Programme na A+ d.s
Inada Company wanda ke gabatar da ayuka
a fannoni daban-daban
Na karantar da littafai kusan dari a rayuwata
a fagage da fannoni mabanbanta
Na gabatar da Laccoci daban-daban a gida
Najeriya da kasashen ketare
Na fassara littafai na musulunci masu yawa
Nayi Tahqiqin littafai dadama
Na gina cibiya mai suna Daarul-Hadeethis
Salafiyyah Zaria Nigeria(DHSN) wadda a
karkashinta akwai makarantu kamar:
Albaniy Science International Academy(Pre-
Nursery, Nursery, Primary da Secondary) na
bangaren maza dana bangaren mata
Daaru bn Katheer Litahfeezil Qur'an
Sheikh Nasiruddenil Albaniy College of
Higher Islamic Studies
Na fara gina Jami'a mai suna Albaniy
University of Informations and
Communications Technology
Na fara gina gidan marayu
Na samar da inda zan gina Asibiti
Na samar da inda zan gina gidan rediyo da
talbijin
Na samar da dakin karatu(library) domin
anfanar malamai da daliban ilmi
Ni mutum ne mai son cigaban al'ummata ta
hanyar ilmi da wayewa
Manzon Allaah(s.a.w) shine Mai gidana
Banayin sassauci ko 'daga 'kafa akan duk
abunda ya sa'bawa Qur'ani da Sunnah abisa
manhajin magabata na kwarai, amma ina
yin hakan tareda duba yanayi, wuri dakuma
halayen mutane
Daga cikin sana'o'ina akwai:
Dinki
Kanikancin computer(computer engineer)
Mashawarci a harkar computer(Computer
Consultant)
Computer Networking
Aikin Jarida
Kasuwanci maban-banta
Aikin rubuce-rubuce, d.s
Duk abunda na assasa a rayuwata da kudina
na samar dasu, domin ban dogara da kowa
ba bayan Allaah mahaliccina sannan sai
sana'o'in danikeyi

Nayi waqafin abubuwan dana assasa
bakidayansu gareni domin anfanar
al'ummar musulmi
Babban manufata shine sharewa musulmai
hawaye gameda matsalolin dasuke fama
dasu na addini da rayuwa a fannoni daban -
daban a karkashin mahanga na addinin
musulunci

Nasan wadanda suka kasheni da wadanda
sukasa a kasheni, amma KASH! bazai yiwu
indawo duniya in bayyanasu ba! Amma
Ubangijinmu yana nan a madakata yana
jiranmu, a inda ranar Alkiyamah zan shako
wuyansu na gurfanar dasu a gaban Allaah
Sarkin sarakuna ince ya tambayesu dan
meyasa suka kasheni...

Ina rokon Allaah yajikaina

Yayi mini rahma

Ya yafe mini kura - kuraina

Yakarbi shahadata

Ya hadani da mai gidana Manzon Allaah
(s.a.w) a Aljannar Firdausi da sauran
musulmai baki daya. Amin amin amin amin amin amin amin amin amin amin amin amin

AMFANIN KARANTA ALQURANI MAI GIRMA (english version)

 


*Suratul Faatiha* protects one from the anger of *Allah.*

*Surah Yaseen* protects one from the thirst of the Day of Judgment

*Suratul Waaqi'ah* protects one from poverty and starvation.

*Surah Mulk* protects one from the punishment of the grave.

*Suratul Kauthar* protects one from the enmity of the enemy.

*Suratul Kaafiroon* protects one from kufr at the time of death.

*Suratul Ikhlaas* protects one from hypocrisy

*Suratul Falaq* protects one from calamities.

*Suratul Naas* protects one from evil thoughts.

*Advice*
Do not send later. Send it now.
May Allah grant success to every one who reads it and sends it. *Ameen*

#copy

 

ABUBUWAN DA YAKAMATA KIBARI YAYIMIKI KO KICE YAYIMIKI

 


ABUBUWAN DA YAKAMATA KIBARI YAYIMIKI KO KICE YAYIMIKI

1) Kunshi
Ki koya masa yanda ake sa lallai a hannu don wataran yasa miki
Idan kina son nail polish sanda duk kike menses sai ki bashi ya shafa miki.

2) Bashi dankunne ya sa miki. Ko agogo ko awarwaro ko ma sarka.

3) Juya ya zuge miki zif
Sama ko kasa.

4) Inkin wanki kanki, ya bushe. Hada hair oil ki bashi yai miki oiling gashin

5) Bashi mai ya shafa miki a baya. Musamman idan man mai kamshi ne.

6) Ki bari yaga yanda kike kwalliya. Musamman a ina kike sa turare a jikinki.
A wuya, a kasan guiwarki, a hammata,abayan kunne da cibiya. Shafe duk jikinki.
Ki bari ya gani.: Abubuwan da ya kamata
Kuyi tare.

At least sau daya kuyi sallah tare.

1) Kuci abinci tare

2) Ku yiwa juna karatu ko da wani bangare ne a jarida ko dan labari.

3) Cuddle up don yana kara shakuwa.

4)Share your ear piece.
Wani dan peace of wa'azi kika samo ko joke ko ma wata love song.
Sa masa kunne daya, kisa kunne daya kuji tare.

5) Help him shave. Amma don Allah karki yanke shi.
Be very gentle. Show tenderness and love.

6) Yanke masa farce ki bashi foot bath.
Musamman idan a gajiye yake.

7)And jefi jefi don karawa kauna da armashi
Have a pillow fight
Kuyi wasan lido ko snake and ladders.
Duk abinda zai jawo raha da farin ciki a rayuwarku to kuyi.

Ita rayuwa guda daya ce.
In lokaci ya wuce baya dawowa.
Kuma abinda kuka yi shi kuke tunawa.
So me zai hana ku gina abinda in kun tuna zakuji dadi?
: A ko da yaushe su muke mu shiga ran mazajen mu ba mu bari suyi kyamar mu har ju janye jiki ba.
So muke suyi ta doki da alfahari .
Abubuwan da ko kusa karki yarda kiyi su a gaban miji.

1) Tsifar kai. Musamman idan kitson ki yai tsufa.

2)Daurin kirji, sai dai in wanka kika shiga.
Ko wankan ma, make it stylish & sexy. How?
Ki kama bakin zanin duka biyu, ki daura a kijiki ki kulle, yanda zai zauna das a kirjinki yayi kuma lebatu wic looks very sexy.πŸ˜ƒ

3) Karki yarda ki tauna kashi a gaban miji.
Domin taunar kashi da shan rake kan canza yanayin mutum.
In har kina so kici kashin bari sai bakwa tare.

4) Idan ke maici ce sosai, karki bari miji ya ganki da tulin abinci a gabanki.
Yi kokari kici rabi kafin ya dawo don kinga in zaki kara kadan zaki diba.πŸ˜ƒ

5) Don Allah karki gyatsa ko tusa a gaban miji.
I beg you.

6) Karki sakace ko kaki pls.

7) Karki kuskura kiyi soshe soshe domin Bera ce kawai take wannan halin.
Allah kiyashe mu.πŸ˜ƒ

8) Karki yi karya a gaban sa.

9) Karki zagi, karki kuskura ko da kuwa an bata miki.
Musamman Ashar.
Karki ki yarda.

10) Kar ki kawo masa gulma domin zaki zubar da kimar ki a idonsa.

11) Karki yarda ya ganki da kaushi don Allah... Allah yasa mu dace da fatan zamu gyara rayuwar aure ba abin wasa bane

Copied
Babangida Ibb

SAKO ZUWA GA MAZINATA


ZUWA GA MAZINATA ::YADDA KAYI
HAKA ZA'AYI A NAKA.

Abin mamaki sai kaga mutum
musulmi ya mayar da yin zina babbar
Sana'arsa baya jin kunyar Allah balle
mutanen da take zaune a cikinsu da
yake kallon suna masa kallon mutum
mai mutunci da kima.

Dawa yawan daga cikin masu lalata
tarbiyyar yara mata bayan iyayensu
sun basu cikakkiyar kulawa da
tarbiyya addinin musulunci sai kaga
suna son su kuma su kare yayansu
da kannensu wai kada wani yayi zina
dasu!? wannan ai shine hotiho!.
Wallahi Idan kayi zina da yar wani to
ka tabbatar ko aljanu ka sanya suna
gadinta to sai anzo har cikin falon
gidanka yadda kake hutawa ayi zina
da yarka ta cikinka ko kanwarka.

Sannan Idan kana da hankali ai ya
kamata kayi tunanin wacce zakayi
zina da ita kanwar wani ce, yayar
wani ce, yar wani ce , matar wani ce,
kuma uwar wani ce fa?.
yanzu kana so ayi zina da matarka?
kana so ayi zina da yarka?
kana son ayi zina da uwaka?
kana son ayi zina da yayarka ko
kanwarka?

Tabbas na San ko shakka babu
amsarka zata zama baka so ayi
dasu !, tunda hakane to kai me yasa
zaka je ka lalata tarbiyyar da sukayi
mata?
lokacin da za kayi zina da yarinya sai
ka cire mata Riga , danuwana ka tuna
cewa mahaifinta ne ya saya mata
don kare mata mutuncinta amma kai
kuma sai ka bude mata saboda
rashin imani?.

Idan ka zama mazinaci to ka lalata
zuriyarka gaba daya domin kuwa
Annabi saw ya tabbatara mana da
cewa ana gadon zina daga wajen
mahaifi ko mahaifiya kaga kenan dole
acikin yayanka a samu mazinaci ko
mazinaciya ko baka so kuwa kuma
komai tsarin daka bayar kuwa.
Sannan ka gane zina bata buya ko
Ba a garinku kakayi ba indai kai
mazinaci ne wallahi sai Allah ya tona
maka asiri kowa ya gane halinka.

Ni Sirajoa Isah Yunusa ina rokon
Allah da dukkanin sunayensa
kyawawa ya karemu daga fada cikin
wannan musifar gaba dayan wadanda
suka shiga cikinta kuma manya da
yara Ubangiji idan masu shiryuwane
Ka shiryesu Idan Ba masu shiryuwa
bane Allah ka nisanta su daga
garemu da yayanmu da kannenmu da
matanmu kamar yadda ka nisanta
gabas da yammma.

 

Thursday, April 16, 2020

TARBIYYAR YARA



TARBIYYAR YARA A MUSULUNCI. //1
TARBIYYA hakkine da Allah (SWT) ya wajabtawa Iyaye suyi ga 'ya'yansu, kamar yadda ya wajabtawa 'ya'ya yin biyayya ga iyayensu.
Kamar yadda muka sani, 'ya'ya kyautace (Ni'imace) daga Allah da yake bayar da ita ga wanda yaga dama, kuma Amanace da Allah ya dankata a hannun iyaye. Sabida haka Iyayen da suka kyautata wajen tarbiyyantar 'ya'yansu da ladabtar dasu bisa koyarwar Musulunci, to sun sauke wannan amanar, Wadanda kuma suka yi sakaci kuma suka takaita wajen yi musu tarbiyya to sun tozarta wannan Amanar.
Allah Ta'ala yace: " Ya ku wadanda su kayi imani, ku tsare kawunanku da iyalanku daga wuta, wacce mutane da duwatsu ne makamashinta... "
(Tahrim: 6).
Annabi (SAW) yana cewa a wani hadisi:
" Dukkanninku masu kiwone kuma ababan tambayane dangane da kiwon da aka baku, shugaba me kiwone (dangane ga talakawansa) kuma abin tambayane dangane da kiwon da aka bashi, mutum me kiwone dangane ga iyalinsa kuma abin tambayane dangane da kiwon da aka bashi."
Bukhari da Muslim.
Akwai wasu hanyoyi wadanda idan muka bisu zasu taimaka mana da yardar Allah wajen Tarbiyyar 'yayanmu, daga cikinsu akwai:
1. MU ZABAWA 'YA'YANMU UWA TA GARI.
Auren mace tagari muhimmin lamarine dake taimakawa wajen tarbiyyar 'ya'ya, domin uwa ita ce makaranta ta farko da yaro ke daukar darasi a cikinta, kuma halaye da dabi'un uwa suna tasiri matuka ga 'ya'yanta, sabida hakane shari'a ta kwadaitar damu wajen auren mace tagari ma'abociyar addini.
Annabi (SAW) yana cewa: " Ana auren mace sabida abubuwa guda 4; dukiyarta, da kyawunta, da daukakarta, da addininta. ka zabi ma'abociyar addini, sai hannunka yayi albarka."
Bukhari da Muslim.
Abu ne mai muhimmanci ga wanda yake da niyyar yin aure ya dage da addu'a akan Allah ya azurtashi da samun mace tagari, kuma yayi "istikhara" wato neman shawarar (zabin) Allah kafin auren, ya kuma nemi shawarar bayin Allah mutanen kirki, sannan yayi kokari wajen yin bincike akan nagartar yarinyar da kuma iyayenta, ya kuma fawwala al'amuransa zuwa ga Allah SWT.
Sannan kuma ya zama wajibi abi hanyoyin da Shari'a ta tsara wajen neman aure, kuma a nisanci sabawa Allah da sunan murna ko farinciki a yayin aure, wannan zai sa Allah Ta'ala ya sanya Albarka a cikin auren da kuma zuriyar da za a samu ta dalilin wannan auren.
2. ROKON ALLAH YA BAKA ZURRIYYA TA GARI.
Wannan dabi'ace ta Annabawa da Manzanni da bayin Allah salihai. Kamar yadda Allah ya bamu labari a kissar Annabi Zakariyya (AS), yake cewa: " A yayin nan Annabi Zakariyya ya roki Ubangijinsa, yace: ya Ubangiji ka bani kyauta daga gareka ta zuriyya tsarkakakkiya, hakika kai mai amsar addu'ane."
(Ali-Imran: 38)
A wata ayar kuma Allah ya bamu labarin salihan bayinsa, daga cikin siffofinsu suna addu'ar Allah ya basu mata da 'ya'ya nagari, yake cewa:
" Wadannan da suke cewa ya Ubangijinmu ka bamu kyauta daga matayenmu da zuriyyarmu abinda idanuwanmu za suyi sanyi dasu, kuma ka sanyamu mu zama shugabanni ga masu tsoron Allah."
(Al-furqan: 74)
Wannan ya nuna mana muhimmancin addu'a da rokon Allah wajen samun 'ya'ya nagari kasancewar har Annabawan Allah da Salihai sun yi irin wannan addu'ar.
Allah ya bamu ikon yiwa 'ya'yayenmu tarbiyya da ladabdar dasu bisa koyarwar Kur'ani da Sunnah,

Thursday, March 26, 2020

GANIN GASHIN CORONA VIRUS




GASHIN_CORONAVIRUS..
ALHAMDULILLAH
Na kammala dukkanin binciken da zanyi akan wannan GASHIN... Kuma zahiri Naga GASHIN agurare MAban-banta....
A'INA NAGA GASHIN KUMA MAI NE NE SHAIDA.!
Dafarko na Dauko ALQUR'ANI NAH ,na duba bangani ba, Na sake dauko wani ALQUR'ANI NAH Wanda bancika amfani dashi ba....
Ina daukowa Naduba suratul Baqara banganiba har qarshe Bangani ba...
Wanda a yanda ake ya'da labarin a suratul baqara kawai ake gani....
Na cigaba da budewa Allah cikin ikonsa Na duba suratul Al-imrana, na samu GASHIN ,na duba nisa'i na samu, daga nan WALLAHI kusan ko wace sura na bude sai na samu....
..
..Dahaka ne nadinga dauka daya bayan daya INA taarawa ,wani na iya dauka ,wani Kuma inna dauko sai ya fadi saboda sirantar sa..
SHIN ACIKIN ALQUR'ANI KAWAI AKE GANIN GASHIN KO HAR A WASU LITTAFAN...?
Nayi mamaki da afkuwar hakan ainun....
Sai nayi wani tunani nace bari na duba littafan BOKO... Irinsu Textbooks da Novel da sauran makamantan su.....
Na je na dauko wani tsohon littafi na,Wanda aka rubuta shi,Akan tarihin Samun 'YANCIN NIGERIA ,Na mahaifi NAH na duba Shima na samu ziri daya nagashin Wanda na iya daukowa...sauran sunyi siranta dayawa bazasu dauku ba.....!
SHIN WANNAN GASHIN YAYA KALARSA TAKE..?!
GASHIN zaku sameshi kamar zare ,siriri ,BAQI DA FARI AKWAI KUMA JAA ...
KAMAR YANDA NAGA RUBUTUN WANI DAN UWA YA TABBATARDA CEWAR WANNAN ZAREN ZA'A IYA SAMUNSHI AKOWANE IRIN LITTAFI....DALILIN SAMUWAR SA ,DAGA PUBLISHING COMPANY NE(MA MAIKATAR BUGA LITTAFAI)
SUBHANALLAH..!!!
SHINE WASU 6ARA GURBIN MUSULMI SUKE AMFANI DA WANNAN DAMAR WAJEN KIRKIRAWA ANNABI S.A.W QARYA...
ANNABI S.A.W "YACE DUK WANDA YAYI MINI QARYA DA GANGAR TO YA TATTALI MAZAUNINSA A WUTA...
*BAYAN HAKA GA WULAQANTA LITTAFIN ALLAH.....
Allah kadai yasan adadin mutanen dasuke da janaba ko Haida ko qananun yara marasa tsarki suka dinga daukar ALQUR'ANI..
*AMADADIN A KOMA GA ALLAH AMMA SAI AKE QOQARIN JANYO MANA WATA MASIFAR...
Wal'iyazuBilLAH....
ALLAH YAMANA TSARI DAGA 'YAN DANFARAR IMANI...
ALLAH KADAI YASAN ADADIN MUTANEN DA SUKA JIQA ZARE (DASUNAN GASHI) SUKASHA...
MUTANE IDON SU YARUFE SUNA TUNANIN AKWAI WANDA YA ISA YADAUKE MANA WANNAN MUSIBAR TA CORONAVIRUS BAYAGA ALLAH...?
KO KUN MANTA SHEKARU DASUKA SHUDE...
AKACE MANA ANA GANIN DODON BANGO...
ALLAH YAJIQAN WANI MALAMIN AHLUSSUNAH BADAN YA MUTUBA....
Alokacin muna cikin uqubar wani shugaba,MALAMIN YACE " tunda ana ganin shi shi DODON bangon mai yasa baza'a fa'da masa ba yazo ya murqushe mana wannan azzalumim shugaban In gaskiya ne...
HAka wata yarinya a unguwar mu ,taxi ta qoshi yayi barci ta farka wai sai kawai taga DODON BANGO acikin dakinta....
MUTANE NATA tururuwar zuwa gani ....
Alokacin wasu suce sun ganshi bakai at are dashi ajikin BANGO wasu suce sunganshi complete da sanda.... Alokacin idan mutum bai samu ikon ganinsa ba sai ace wai bashida rabo....
Hatta 'YAN jarida saida suka kawo mata ziyara alokacin.....
...BAyan wasu kwanaki Ashe wai TAMBOTSAN samankanta ne keyi mata gizo..da sauran 6attatun mutanenta.....
HAKA AKAYI ASHEKARUN BAYA DASUKA SHU'DE AKAN EBOLA...
Aka dinga YA'DA jita-jitan shan ruwan gishiri da kuma wanka dashi....
MUTANE suka manta Allah acikin ZUKATANSU....
Sanadin shan ruwan gishiri yayi sanadiyyar Mutuwar MUTANE da da-ma wasu kuma sukamkamu da cututtuka....
Da aka tsananta bincike. Ashe wai PASTOR ne yayi MAFARKI......
....WANNAN KARON KUMA SAI AKAZO DA SABON SALON YAUDARA DAKUMA DAMFARAR IMANI.....
Wanda WALLAHI MUTANE dayawa suntafi ahakan..
..★TO BARA KUJI KU MASU SHAN RUWAN GASHI(ZARE) IDAN SANADIN KAMUWA DA WASU CUTUKAN NE YAZO ALLAH YABADA SA'A★
YAYIN DA MUTANE SUKA MANTA ALLAH AZUKATANSU SAI ALLAH YA BARSU DA IYA WARSU...
ALLAH YASA MUTANE SU HANKALTA...!
YAA! UBANGIJIN MU KARKA KA-MAMU DA LAIFINDA WASU WAWAYE DAGA CIKIN MU SUKE AIKATAWA....
#GA_HUJJA_NAN_NAKAWO_MANA_AWANNAN_HOTON...
#KUNSAN_ITA_HUJJA_ #TAKOBIN_AHLUSSUN_NAH
Safeeyyah Suleiman Umar