Thursday, October 29, 2020

MAFARKINAH JIYA DA DADDARE

 




 ( MAFARKINAH JIYA DA DADDARE)💞
Ku biyoni kusha Labari
💞💓💞

Annabi S.A.W Ya-ce " Mafarki Mai kyau daga Allah ne..
...Mafarki Mara kyau daga shaiɗan ne..

Malamai sunyi ƙarin bayani Game da mafarki Mai kyau .. zaka iya bayyanawa..
Mafarki mara kyau kuma idan kayi ka nemi tsari daga shaiɗan kayi tofi sau uku.. kuma mutum ya ka-me bakinsa basai ya bayyana ba..

Alhamdulillah 🙏😍
Sabda Wannan Dalilin ne ,nakeso bayyana mafarkin danayi daren jiya.
.
Tare da wata baiwar Allah,wacce friend dita ce.. tsawon shekaru da dama a wannan kafa ta Sa-da zumunta...
Ban taɓa ganinta ido-da ido ba,..

WALLAHI BAN SANTA DA WANI AIKI BA, FA-CE AYYUKAN ALKHAIRI A WANNAN KAFA TA FACEBOOK SOSAI,WAJEN DA'AWA ,FAƊAKARWA ..
ALLAH YASAKA MATA DA ALKHAIRI.

Allah cikin ikon sa,Ƙudirar sa.., jiya nayi Mafarki da ita Malama Faridah Bintu Salis ,😍

Na Gammu acikin wani babban masallaci.., Masallacin yayi kama da masallacin juma'a, Muntara Mata dayawa Bila adadin .., masallacin yacika MaQil da Mata..

Mu kuma muna kan wasu kujeru a saman step.. ko wacce da Alarammiyyar ta, Nafara tafsirin Alkur'ani Mai Girma acikin سورة عبس
🎤🎤🎤

Alarammiyya ta wacce bansan ko wacece ba a mafarkin tana jaa min BaQee Ni kuma ina FASSARAWA... Idan nayi nagaji sai Malama #Faridah_Bintu_Salis ta ƙarɓa taci gaba da tafsirin Ana jaa mata baQee ..🎤🎤
Mata na sauraren tafseerin Alkur'ani mai Girma daga bakunan mu..🎤🎤🎤

Agefe kuma wani Malamin Islamiyyar mu ne a Zamfara..
Malam Muhammad Sani Abdulkarim Gusau.
Shugaban makarantar مدرسة تربية الإسلام تدون ودا غسو.

Shiyake Guiding din mu idan wata kalma ,fassarar ta tashige mana yafassara mana..

Ana cikin haka Ina tafseerin sai wasu kalmomi suka shige mun , namanta fassarar su..
Kalmar عبد
(Abdu)

Da kuma عربا
(Urbaa)

Sai na tambayi Malama #Faridah fassarar su sai tace wallahi Malama nima fassara ta shige mun...

Sai na tambayi wannan malamin namu na Islamiyyah ,Sai Ya tuna mana fassarar kalmomin ,muka ci gaba da tafseerin Abun mu..
😍
Anan Nafarka da Dadda ɗan Mafarkinah na daren jiya..
Around 2:10am Na dare...
Wallahi sabda farin ciki nakasa komawa barci,ina ta tasbihi ga Allah, Na dauki tsawon lokaci kafin wani baccin Ya daukeni..

Alhamdulillah 🙏
Allah nake Roko Ya tabbatar da wannan Mafarkin nawa..

Annabi S.A.W Yace"Mafi Alkhairin ku,Wanda Ya koyi ALKUR'ANI KUMA YA KOYAR DASHI."

Yaa! Ka bamu ilimin wannan littafin naka,
Mu amfanar da Al'umma dashi..
YAa HAYYU Yaa QAYYUM.

Dukkanin wani ko wata da Take da babban Buri akan Littafin ka Mai Tsarki..
Allah ka sauƙaƙe mana hanyar koyon shi ,Muhaddaceshi,Mu amfanar da Al'umma dashi..

YAa HAYYU Yaa QAYYUM 🤲
Allah kasanYa Alƙur'ani yacecemu Ranar Gobe kiyama.

Ina miki Fatan Alkhairi.
Malama #Farida_Bintu_Salis

Safeeyyah Suleiman Umar
25-Oct.2020.

No comments:

Post a Comment