Thursday, October 29, 2020

GWALA-GWALAN MALLAKAR ZUCIYAR MAIGIDA

 

 


GWALA-GWALAN MALLAKAR ZUCIYAR MAIGIDA

TSABTA DA KWALLIYA

Lallai kowani Namiji yana son matarsa ta kasance a koda yaushe cikin tsabta da kwalliya, ta yadda ba zai ga wasu matan a waje ba sunyi kwalliya su burge shi ba, amma a yau mun wayi gari da yawa daga cikin Mata suna yin sakaci da tsabta da kwalliya ta yadda matan waje masu iya kwalliya da ado da tsabta su ke janye zuciyar mazajensu.

Saboda haka 'Yar uwa ki tunani kuma ki sani ke ba mummuna ba ce, ki tashi tsaye ki zama koda yaushe cikin tsabta da kwalliya. Ki kasance ga mijinki tamkar kyakkyawar fulawa mai furanni iri-iri na kyau tare da shekin iska mai kamshi a tare dake da kuma kyakkyawar shiga ta kaya irin mai jan hankalin miji.

GWALA-GWALAN MALLAKAR ZUCIYAR MAIGIDA

IYA RARRASHIN MIJI

Tabbas rayuwar aure rayuwace ta haƙuri, dole wata rana za a samu saɓani. Shi dai rarrashi abu ne da mazaje suke jin daɗinsa a zukatansu, musamman kuma ace mace ta san hanyoyi daban-daban na tarairayar miji.
Macer da ta iya rarrashin miji ita ce wacce in ta vatawa mijinta rai kuma ta ga alamun haka a fuskarsa, takan je kusa da shi ta zauna ta bashi hakuri ta hanyar amfani da wasu kalmomi masu taushi masu tsada.

Shiyasa Nana Khadijah {r.a} ta yiwa matan Duniya fincinkau wajen iya rarrashin miji kamar yadda ya tabbata a tarihi. A lokacin da Manzon Allah {s.a.w} ya dawo daga Kogo cikin firgici, amma saboda kwarewarta wajen iya rarrashin miji sai ta nuna masa cewa ai babu abin da zai sameshi in sha Allah domin yana sada zumunta da sauransu.

Abin tambayata anan shin matan yanzu in su ka ɓatawa mazajensu rai ko suka dawo cikin bacin rai haka suke musu?

Copied/Dan uwanku a Musulunci: Yusuf Lawal Yusuf

GWALA-GWALAN MALLAKAR ZUCIYAR MAIGIDA

KISHIN MIJI

Sannunku da aiki ya ku mabiya wannan rubutu nawa, a yau zan ci gaba da lissafo muku wadannan gwala-gwalan da nike bayani a kansu. Hanya ta gaba da Mace za tabi domin mallake zuciyar maigida shine: KISHIN MIJI. Duk Mace ta gari tana kishin mijinta, ita ko kalmar "KISHI" kamar yadda Sheikh Basheer Lawal Muhammad Zaria ya anbata a wani rubutu nasa ya ce: kalma ce mai wuyar fassarawa amma za mu iya cewa: Kishi wani abu ne a zuciya da ke sa a damu matuƙa da abin da ake so, kuma a ƙi alfarmar wannan abu ta zube, kuma ake kaffa-kaffa da shi, da gudun kar wani ya rabauta da shi fiye da shi mai sonsa.

Saboda haka, ya ke ƴar uwa ki zama mai kishin mijinki a ko ina yake, ta hanyar nuna damuwarki lokacin da kika ga ya shiga wani hali, idan bai da lafiya kiji kamar kece baki da lafiya idan zai fita aiki ki rakashi, idan ya isa wajen aikin ki kirashi bayan ya dauki wayar sai kice: Jarumina, ko Hasken idanuna, ko baban wane ina fatan ka isa lafiya?.

ƁOYE ABIN SONKI SHINE KISHINSA, KISHINSA KUMA ALAMAR SONSA NE.

Zamu dakata anan sai mun hadu a rubutu na gaba in sha'allah.

Copied Yusuf Lawal Yusuf

 

 

No comments:

Post a Comment