Thursday, October 29, 2020

SHEIK ALBANY (RAHIMAHULLAH)


 

Sunana Muhammad Auwal
Sunan Mahaifina Adam
Sunan mahifiyata Saudah
Abu - Abdirrahman shine Alkunyana
Albaniy shine Lakabina
An haifeni a Anguwan Muciya Sabon Garin
Zaria a shekarar 1960
Nayi makarantar Allo har nayi sauka
Na koyi littafan da akeyi a zaure na fiqhu
dana lugah da Adab
Nayi karatu a wurin manyan malamai
mabanbanta a kasata Najeriya da kasashen
waje inda na koyi Qur'ani da dukkan
kira'o'insa, Hadisi da musdalah dinsa, Tafsiri
da Usul dinsa, Tareekh da usul dinsa,
Aqeedah da Manhaj da usul dinsu, Harshen
larabci da fannoninsa, Fiqh da Usul da
Qawa'id dinsa, d.s
Nayi makarantar firamare a Sabon Garin
Zaria
Nayi Sakandire a kwalejin Barewa Zaria
Nayi Diploma akan:
Law
Computer Science
Mass Communication
Hausa Language
Nayi Degree akan ICT
Nayi Masters akan Islamic Studies
Ni Professional Jounalist ne
Ni Certified Microsoft Engineer ne
Ni Linguistic ne
Na karanci Library Science
Nayi Programme na N+ akan Computer
Nayi Programme na A+ d.s
Inada Company wanda ke gabatar da ayuka
a fannoni daban-daban
Na karantar da littafai kusan dari a rayuwata
a fagage da fannoni mabanbanta
Na gabatar da Laccoci daban-daban a gida
Najeriya da kasashen ketare
Na fassara littafai na musulunci masu yawa
Nayi Tahqiqin littafai dadama
Na gina cibiya mai suna Daarul-Hadeethis
Salafiyyah Zaria Nigeria(DHSN) wadda a
karkashinta akwai makarantu kamar:
Albaniy Science International Academy(Pre-
Nursery, Nursery, Primary da Secondary) na
bangaren maza dana bangaren mata
Daaru bn Katheer Litahfeezil Qur'an
Sheikh Nasiruddenil Albaniy College of
Higher Islamic Studies
Na fara gina Jami'a mai suna Albaniy
University of Informations and
Communications Technology
Na fara gina gidan marayu
Na samar da inda zan gina Asibiti
Na samar da inda zan gina gidan rediyo da
talbijin
Na samar da dakin karatu(library) domin
anfanar malamai da daliban ilmi
Ni mutum ne mai son cigaban al'ummata ta
hanyar ilmi da wayewa
Manzon Allaah(s.a.w) shine Mai gidana
Banayin sassauci ko 'daga 'kafa akan duk
abunda ya sa'bawa Qur'ani da Sunnah abisa
manhajin magabata na kwarai, amma ina
yin hakan tareda duba yanayi, wuri dakuma
halayen mutane
Daga cikin sana'o'ina akwai:
Dinki
Kanikancin computer(computer engineer)
Mashawarci a harkar computer(Computer
Consultant)
Computer Networking
Aikin Jarida
Kasuwanci maban-banta
Aikin rubuce-rubuce, d.s
Duk abunda na assasa a rayuwata da kudina
na samar dasu, domin ban dogara da kowa
ba bayan Allaah mahaliccina sannan sai
sana'o'in danikeyi

Nayi waqafin abubuwan dana assasa
bakidayansu gareni domin anfanar
al'ummar musulmi
Babban manufata shine sharewa musulmai
hawaye gameda matsalolin dasuke fama
dasu na addini da rayuwa a fannoni daban -
daban a karkashin mahanga na addinin
musulunci

Nasan wadanda suka kasheni da wadanda
sukasa a kasheni, amma KASH! bazai yiwu
indawo duniya in bayyanasu ba! Amma
Ubangijinmu yana nan a madakata yana
jiranmu, a inda ranar Alkiyamah zan shako
wuyansu na gurfanar dasu a gaban Allaah
Sarkin sarakuna ince ya tambayesu dan
meyasa suka kasheni...

Ina rokon Allaah yajikaina

Yayi mini rahma

Ya yafe mini kura - kuraina

Yakarbi shahadata

Ya hadani da mai gidana Manzon Allaah
(s.a.w) a Aljannar Firdausi da sauran
musulmai baki daya. Amin amin amin amin amin amin amin amin amin amin amin amin

No comments:

Post a Comment