ZUWA GA MAZINATA ::YADDA KAYI
HAKA ZA'AYI A NAKA.
Abin mamaki sai kaga mutum
musulmi ya mayar da yin zina babbar
Sana'arsa baya jin kunyar Allah balle
mutanen da take zaune a cikinsu da
yake kallon suna masa kallon mutum
mai mutunci da kima.
Dawa yawan daga cikin masu lalata
tarbiyyar yara mata bayan iyayensu
sun basu cikakkiyar kulawa da
tarbiyya addinin musulunci sai kaga
suna son su kuma su kare yayansu
da kannensu wai kada wani yayi zina
dasu!? wannan ai shine hotiho!.
Wallahi Idan kayi zina da yar wani to
ka tabbatar ko aljanu ka sanya suna
gadinta to sai anzo har cikin falon
gidanka yadda kake hutawa ayi zina
da yarka ta cikinka ko kanwarka.
Sannan Idan kana da hankali ai ya
kamata kayi tunanin wacce zakayi
zina da ita kanwar wani ce, yayar
wani ce, yar wani ce , matar wani ce,
kuma uwar wani ce fa?.
yanzu kana so ayi zina da matarka?
kana so ayi zina da yarka?
kana son ayi zina da uwaka?
kana son ayi zina da yayarka ko
kanwarka?
Tabbas na San ko shakka babu
amsarka zata zama baka so ayi
dasu !, tunda hakane to kai me yasa
zaka je ka lalata tarbiyyar da sukayi
mata?
lokacin da za kayi zina da yarinya sai
ka cire mata Riga , danuwana ka tuna
cewa mahaifinta ne ya saya mata
don kare mata mutuncinta amma kai
kuma sai ka bude mata saboda
rashin imani?.
Idan ka zama mazinaci to ka lalata
zuriyarka gaba daya domin kuwa
Annabi saw ya tabbatara mana da
cewa ana gadon zina daga wajen
mahaifi ko mahaifiya kaga kenan dole
acikin yayanka a samu mazinaci ko
mazinaciya ko baka so kuwa kuma
komai tsarin daka bayar kuwa.
Sannan ka gane zina bata buya ko
Ba a garinku kakayi ba indai kai
mazinaci ne wallahi sai Allah ya tona
maka asiri kowa ya gane halinka.
Ni Sirajoa Isah Yunusa ina rokon
Allah da dukkanin sunayensa
kyawawa ya karemu daga fada cikin
wannan musifar gaba dayan wadanda
suka shiga cikinta kuma manya da
yara Ubangiji idan masu shiryuwane
Ka shiryesu Idan Ba masu shiryuwa
bane Allah ka nisanta su daga
garemu da yayanmu da kannenmu da
matanmu kamar yadda ka nisanta
gabas da yammma.
No comments:
Post a Comment