Thursday, October 29, 2020

SUNNAH LEKA GIDAN KOWA

 


NAZIYARCI BABBAN MASALLACHIN AUCHI

Yaa Allah ka ƙara Daukaka SUNNAH ..
Allah ka Tsare mana 'Yan agajin mu,Da Maluman mu Na SUNNAH.🤲

JIYA Na halarci Wani Babban Masallacin juma'a a garin Ekabigbo AUCHI, (Edo State)
Abun Ya burgeni Yanda Na ga Yara mata da. ,'yan mata da kuma tsofaffi Mata sun cika Masallaci Domin Sallatar Juma'a. Abun Ya burgeni Wallahi...

Gefe kuma Ga SOJOJIN SUNNAH JIBWIS , wato 'Yan Agaji Mata da Maza ..

Alhamdulillah 🙏
Duk da Kasancewar su Garine da 'Yan Bidi'a suka Yawaita, Amma hakan bai hana wasu Halartar wajen Ibada ba...

YAA! ALLAH KA ƘARA CUSA MUSU SON SUNNAH ACIKIN ZUKATANSU...

YA RABBI KA ƊAUKI RAYUKAN MU MUNA MUSULMAI AHLUSSUNNAH..
ALLAH KA AMSHI IBADUN MU..

ALLAH KA SAKAWA IYAYEN MU DA ALKHAIRI..
ALLAH ƘARA MUSU LAFIYA DA RAYUWA MAI ALBARKA...
ALLAH KAYI MUSU SAKA-MAKO DA GIDAN ALJANNAH..

WAƊANDA SUKA RASU ALLAH KA HASKAKA MUSU MAKWANCINASU ,ALLAH KASANYA ALJANNAH FIRDAUS TA ZAMA MAKOMA AGARESU..🤲

AMEEN YA HAYYU YAA QAYYUM.👏

Safeeyyah Suleiman Umar
24-Oct.2020

BA MUTUWARCE ABAR TASHIN HANKALI BA

 


Bafa Mutuwar bace Abar firgice da tashin hankali...

Abunda bawa zai tarar..
Idan yasamu akasin abinda yake tsammani zai riska,bai Samu ba .., Sai Yafaɗa a mummunar Makoma..

Wannan shine Babban Tashin hankali..
Ya Allah ka cire mana Riya acikin Zukatan Mu..
Allah ka tsarkake mana niyyar mu...

Ya Rabb kasanYa dukkanin Abinda zamu Aikata shi,Mu Aikata shi Domin ka Ya Allah..
Allah ka hanamu Aikata Ayyuka Don Ayabemu ko ace Mun iya...

Allah kasa Mudinga Aikata Ayyukan mu Domin ka...
YAa HAYYU Yaa QAYYUM 🤲

Safeeyyah Suleiman Umar
17-Oct-2020

NAGARTA A ZAMANTAKEWA

 


NAGARTA A ZAMANTAKEWA

Tambaya:AssalamualaikiMalama a taimaka mana da yadda za a gyara amarya, na hadin gyara:

Amarya budurwa ce kuma bata da jiki sannan farace ?

Amsa: Wa.alaikumussalam, Da yake fara ce, kuma bata da jiki, sannan budura ce;

Tana bukatarfara gabatar da shan magungunan sanyi, kamar:

Yajin gora
Busassar tafarnuwa
Cittar zabibi
'Yayan zogale
Lawashin albasa
Jan karib

A hada su a busar, a gyara a nika sosai suyi laushi ta rika shan cokalin garin maganin da kunun aya koh kindirmo:

Sauran a nemi mazubi mai rufewa kam a zuba. Sannan a fara gabatar da wannan maganin da an tsaida ranar aure idan dai ba lokaci a ka sanya mai nisa ba.

Domin akasarin 'yan mata suna karatun boko, wanda ke tilasta amfani da bandaki mai kazanta, amfani da audigar mata, koh amfani da bandakin gidan taro:

Sannan 'yan matan mu na zamani baka shaidar su, gwanda a gyara su, domin kada su tafi su dawo.

👌🏼Ke uwa, ke ce dai da ya kamata ki lurar da ita ladabi a wurin miji, da rashin gaddama ga umarnin sa, yi nayi bari na bari, sannan ta kula da tsabta, gyara kwalliya, da sarrafa girki mai dadi mai kuma kyau da kudi 'yan kadan, wanda suna daga cikin sirrikan auratayya.

-------------------------------------
🕋Nisa'us Sunna

Copied

 

GWALA-GWALAN MALLAKAR ZUCIYAR MAIGIDA

 

 


GWALA-GWALAN MALLAKAR ZUCIYAR MAIGIDA

TSABTA DA KWALLIYA

Lallai kowani Namiji yana son matarsa ta kasance a koda yaushe cikin tsabta da kwalliya, ta yadda ba zai ga wasu matan a waje ba sunyi kwalliya su burge shi ba, amma a yau mun wayi gari da yawa daga cikin Mata suna yin sakaci da tsabta da kwalliya ta yadda matan waje masu iya kwalliya da ado da tsabta su ke janye zuciyar mazajensu.

Saboda haka 'Yar uwa ki tunani kuma ki sani ke ba mummuna ba ce, ki tashi tsaye ki zama koda yaushe cikin tsabta da kwalliya. Ki kasance ga mijinki tamkar kyakkyawar fulawa mai furanni iri-iri na kyau tare da shekin iska mai kamshi a tare dake da kuma kyakkyawar shiga ta kaya irin mai jan hankalin miji.

GWALA-GWALAN MALLAKAR ZUCIYAR MAIGIDA

IYA RARRASHIN MIJI

Tabbas rayuwar aure rayuwace ta haƙuri, dole wata rana za a samu saɓani. Shi dai rarrashi abu ne da mazaje suke jin daɗinsa a zukatansu, musamman kuma ace mace ta san hanyoyi daban-daban na tarairayar miji.
Macer da ta iya rarrashin miji ita ce wacce in ta vatawa mijinta rai kuma ta ga alamun haka a fuskarsa, takan je kusa da shi ta zauna ta bashi hakuri ta hanyar amfani da wasu kalmomi masu taushi masu tsada.

Shiyasa Nana Khadijah {r.a} ta yiwa matan Duniya fincinkau wajen iya rarrashin miji kamar yadda ya tabbata a tarihi. A lokacin da Manzon Allah {s.a.w} ya dawo daga Kogo cikin firgici, amma saboda kwarewarta wajen iya rarrashin miji sai ta nuna masa cewa ai babu abin da zai sameshi in sha Allah domin yana sada zumunta da sauransu.

Abin tambayata anan shin matan yanzu in su ka ɓatawa mazajensu rai ko suka dawo cikin bacin rai haka suke musu?

Copied/Dan uwanku a Musulunci: Yusuf Lawal Yusuf

GWALA-GWALAN MALLAKAR ZUCIYAR MAIGIDA

KISHIN MIJI

Sannunku da aiki ya ku mabiya wannan rubutu nawa, a yau zan ci gaba da lissafo muku wadannan gwala-gwalan da nike bayani a kansu. Hanya ta gaba da Mace za tabi domin mallake zuciyar maigida shine: KISHIN MIJI. Duk Mace ta gari tana kishin mijinta, ita ko kalmar "KISHI" kamar yadda Sheikh Basheer Lawal Muhammad Zaria ya anbata a wani rubutu nasa ya ce: kalma ce mai wuyar fassarawa amma za mu iya cewa: Kishi wani abu ne a zuciya da ke sa a damu matuƙa da abin da ake so, kuma a ƙi alfarmar wannan abu ta zube, kuma ake kaffa-kaffa da shi, da gudun kar wani ya rabauta da shi fiye da shi mai sonsa.

Saboda haka, ya ke ƴar uwa ki zama mai kishin mijinki a ko ina yake, ta hanyar nuna damuwarki lokacin da kika ga ya shiga wani hali, idan bai da lafiya kiji kamar kece baki da lafiya idan zai fita aiki ki rakashi, idan ya isa wajen aikin ki kirashi bayan ya dauki wayar sai kice: Jarumina, ko Hasken idanuna, ko baban wane ina fatan ka isa lafiya?.

ƁOYE ABIN SONKI SHINE KISHINSA, KISHINSA KUMA ALAMAR SONSA NE.

Zamu dakata anan sai mun hadu a rubutu na gaba in sha'allah.

Copied Yusuf Lawal Yusuf

 

 

MAFARKINAH JIYA DA DADDARE

 




 ( MAFARKINAH JIYA DA DADDARE)💞
Ku biyoni kusha Labari
💞💓💞

Annabi S.A.W Ya-ce " Mafarki Mai kyau daga Allah ne..
...Mafarki Mara kyau daga shaiɗan ne..

Malamai sunyi ƙarin bayani Game da mafarki Mai kyau .. zaka iya bayyanawa..
Mafarki mara kyau kuma idan kayi ka nemi tsari daga shaiɗan kayi tofi sau uku.. kuma mutum ya ka-me bakinsa basai ya bayyana ba..

Alhamdulillah 🙏😍
Sabda Wannan Dalilin ne ,nakeso bayyana mafarkin danayi daren jiya.
.
Tare da wata baiwar Allah,wacce friend dita ce.. tsawon shekaru da dama a wannan kafa ta Sa-da zumunta...
Ban taɓa ganinta ido-da ido ba,..

WALLAHI BAN SANTA DA WANI AIKI BA, FA-CE AYYUKAN ALKHAIRI A WANNAN KAFA TA FACEBOOK SOSAI,WAJEN DA'AWA ,FAƊAKARWA ..
ALLAH YASAKA MATA DA ALKHAIRI.

Allah cikin ikon sa,Ƙudirar sa.., jiya nayi Mafarki da ita Malama Faridah Bintu Salis ,😍

Na Gammu acikin wani babban masallaci.., Masallacin yayi kama da masallacin juma'a, Muntara Mata dayawa Bila adadin .., masallacin yacika MaQil da Mata..

Mu kuma muna kan wasu kujeru a saman step.. ko wacce da Alarammiyyar ta, Nafara tafsirin Alkur'ani Mai Girma acikin سورة عبس
🎤🎤🎤

Alarammiyya ta wacce bansan ko wacece ba a mafarkin tana jaa min BaQee Ni kuma ina FASSARAWA... Idan nayi nagaji sai Malama #Faridah_Bintu_Salis ta ƙarɓa taci gaba da tafsirin Ana jaa mata baQee ..🎤🎤
Mata na sauraren tafseerin Alkur'ani mai Girma daga bakunan mu..🎤🎤🎤

Agefe kuma wani Malamin Islamiyyar mu ne a Zamfara..
Malam Muhammad Sani Abdulkarim Gusau.
Shugaban makarantar مدرسة تربية الإسلام تدون ودا غسو.

Shiyake Guiding din mu idan wata kalma ,fassarar ta tashige mana yafassara mana..

Ana cikin haka Ina tafseerin sai wasu kalmomi suka shige mun , namanta fassarar su..
Kalmar عبد
(Abdu)

Da kuma عربا
(Urbaa)

Sai na tambayi Malama #Faridah fassarar su sai tace wallahi Malama nima fassara ta shige mun...

Sai na tambayi wannan malamin namu na Islamiyyah ,Sai Ya tuna mana fassarar kalmomin ,muka ci gaba da tafseerin Abun mu..
😍
Anan Nafarka da Dadda ɗan Mafarkinah na daren jiya..
Around 2:10am Na dare...
Wallahi sabda farin ciki nakasa komawa barci,ina ta tasbihi ga Allah, Na dauki tsawon lokaci kafin wani baccin Ya daukeni..

Alhamdulillah 🙏
Allah nake Roko Ya tabbatar da wannan Mafarkin nawa..

Annabi S.A.W Yace"Mafi Alkhairin ku,Wanda Ya koyi ALKUR'ANI KUMA YA KOYAR DASHI."

Yaa! Ka bamu ilimin wannan littafin naka,
Mu amfanar da Al'umma dashi..
YAa HAYYU Yaa QAYYUM.

Dukkanin wani ko wata da Take da babban Buri akan Littafin ka Mai Tsarki..
Allah ka sauƙaƙe mana hanyar koyon shi ,Muhaddaceshi,Mu amfanar da Al'umma dashi..

YAa HAYYU Yaa QAYYUM 🤲
Allah kasanYa Alƙur'ani yacecemu Ranar Gobe kiyama.

Ina miki Fatan Alkhairi.
Malama #Farida_Bintu_Salis

Safeeyyah Suleiman Umar
25-Oct.2020.

SHEIK ALBANY (RAHIMAHULLAH)


 

Sunana Muhammad Auwal
Sunan Mahaifina Adam
Sunan mahifiyata Saudah
Abu - Abdirrahman shine Alkunyana
Albaniy shine Lakabina
An haifeni a Anguwan Muciya Sabon Garin
Zaria a shekarar 1960
Nayi makarantar Allo har nayi sauka
Na koyi littafan da akeyi a zaure na fiqhu
dana lugah da Adab
Nayi karatu a wurin manyan malamai
mabanbanta a kasata Najeriya da kasashen
waje inda na koyi Qur'ani da dukkan
kira'o'insa, Hadisi da musdalah dinsa, Tafsiri
da Usul dinsa, Tareekh da usul dinsa,
Aqeedah da Manhaj da usul dinsu, Harshen
larabci da fannoninsa, Fiqh da Usul da
Qawa'id dinsa, d.s
Nayi makarantar firamare a Sabon Garin
Zaria
Nayi Sakandire a kwalejin Barewa Zaria
Nayi Diploma akan:
Law
Computer Science
Mass Communication
Hausa Language
Nayi Degree akan ICT
Nayi Masters akan Islamic Studies
Ni Professional Jounalist ne
Ni Certified Microsoft Engineer ne
Ni Linguistic ne
Na karanci Library Science
Nayi Programme na N+ akan Computer
Nayi Programme na A+ d.s
Inada Company wanda ke gabatar da ayuka
a fannoni daban-daban
Na karantar da littafai kusan dari a rayuwata
a fagage da fannoni mabanbanta
Na gabatar da Laccoci daban-daban a gida
Najeriya da kasashen ketare
Na fassara littafai na musulunci masu yawa
Nayi Tahqiqin littafai dadama
Na gina cibiya mai suna Daarul-Hadeethis
Salafiyyah Zaria Nigeria(DHSN) wadda a
karkashinta akwai makarantu kamar:
Albaniy Science International Academy(Pre-
Nursery, Nursery, Primary da Secondary) na
bangaren maza dana bangaren mata
Daaru bn Katheer Litahfeezil Qur'an
Sheikh Nasiruddenil Albaniy College of
Higher Islamic Studies
Na fara gina Jami'a mai suna Albaniy
University of Informations and
Communications Technology
Na fara gina gidan marayu
Na samar da inda zan gina Asibiti
Na samar da inda zan gina gidan rediyo da
talbijin
Na samar da dakin karatu(library) domin
anfanar malamai da daliban ilmi
Ni mutum ne mai son cigaban al'ummata ta
hanyar ilmi da wayewa
Manzon Allaah(s.a.w) shine Mai gidana
Banayin sassauci ko 'daga 'kafa akan duk
abunda ya sa'bawa Qur'ani da Sunnah abisa
manhajin magabata na kwarai, amma ina
yin hakan tareda duba yanayi, wuri dakuma
halayen mutane
Daga cikin sana'o'ina akwai:
Dinki
Kanikancin computer(computer engineer)
Mashawarci a harkar computer(Computer
Consultant)
Computer Networking
Aikin Jarida
Kasuwanci maban-banta
Aikin rubuce-rubuce, d.s
Duk abunda na assasa a rayuwata da kudina
na samar dasu, domin ban dogara da kowa
ba bayan Allaah mahaliccina sannan sai
sana'o'in danikeyi

Nayi waqafin abubuwan dana assasa
bakidayansu gareni domin anfanar
al'ummar musulmi
Babban manufata shine sharewa musulmai
hawaye gameda matsalolin dasuke fama
dasu na addini da rayuwa a fannoni daban -
daban a karkashin mahanga na addinin
musulunci

Nasan wadanda suka kasheni da wadanda
sukasa a kasheni, amma KASH! bazai yiwu
indawo duniya in bayyanasu ba! Amma
Ubangijinmu yana nan a madakata yana
jiranmu, a inda ranar Alkiyamah zan shako
wuyansu na gurfanar dasu a gaban Allaah
Sarkin sarakuna ince ya tambayesu dan
meyasa suka kasheni...

Ina rokon Allaah yajikaina

Yayi mini rahma

Ya yafe mini kura - kuraina

Yakarbi shahadata

Ya hadani da mai gidana Manzon Allaah
(s.a.w) a Aljannar Firdausi da sauran
musulmai baki daya. Amin amin amin amin amin amin amin amin amin amin amin amin

AMFANIN KARANTA ALQURANI MAI GIRMA (english version)

 


*Suratul Faatiha* protects one from the anger of *Allah.*

*Surah Yaseen* protects one from the thirst of the Day of Judgment

*Suratul Waaqi'ah* protects one from poverty and starvation.

*Surah Mulk* protects one from the punishment of the grave.

*Suratul Kauthar* protects one from the enmity of the enemy.

*Suratul Kaafiroon* protects one from kufr at the time of death.

*Suratul Ikhlaas* protects one from hypocrisy

*Suratul Falaq* protects one from calamities.

*Suratul Naas* protects one from evil thoughts.

*Advice*
Do not send later. Send it now.
May Allah grant success to every one who reads it and sends it. *Ameen*

#copy

 

ABUBUWAN DA YAKAMATA KIBARI YAYIMIKI KO KICE YAYIMIKI

 


ABUBUWAN DA YAKAMATA KIBARI YAYIMIKI KO KICE YAYIMIKI

1) Kunshi
Ki koya masa yanda ake sa lallai a hannu don wataran yasa miki
Idan kina son nail polish sanda duk kike menses sai ki bashi ya shafa miki.

2) Bashi dankunne ya sa miki. Ko agogo ko awarwaro ko ma sarka.

3) Juya ya zuge miki zif
Sama ko kasa.

4) Inkin wanki kanki, ya bushe. Hada hair oil ki bashi yai miki oiling gashin

5) Bashi mai ya shafa miki a baya. Musamman idan man mai kamshi ne.

6) Ki bari yaga yanda kike kwalliya. Musamman a ina kike sa turare a jikinki.
A wuya, a kasan guiwarki, a hammata,abayan kunne da cibiya. Shafe duk jikinki.
Ki bari ya gani.: Abubuwan da ya kamata
Kuyi tare.

At least sau daya kuyi sallah tare.

1) Kuci abinci tare

2) Ku yiwa juna karatu ko da wani bangare ne a jarida ko dan labari.

3) Cuddle up don yana kara shakuwa.

4)Share your ear piece.
Wani dan peace of wa'azi kika samo ko joke ko ma wata love song.
Sa masa kunne daya, kisa kunne daya kuji tare.

5) Help him shave. Amma don Allah karki yanke shi.
Be very gentle. Show tenderness and love.

6) Yanke masa farce ki bashi foot bath.
Musamman idan a gajiye yake.

7)And jefi jefi don karawa kauna da armashi
Have a pillow fight
Kuyi wasan lido ko snake and ladders.
Duk abinda zai jawo raha da farin ciki a rayuwarku to kuyi.

Ita rayuwa guda daya ce.
In lokaci ya wuce baya dawowa.
Kuma abinda kuka yi shi kuke tunawa.
So me zai hana ku gina abinda in kun tuna zakuji dadi?
: A ko da yaushe su muke mu shiga ran mazajen mu ba mu bari suyi kyamar mu har ju janye jiki ba.
So muke suyi ta doki da alfahari .
Abubuwan da ko kusa karki yarda kiyi su a gaban miji.

1) Tsifar kai. Musamman idan kitson ki yai tsufa.

2)Daurin kirji, sai dai in wanka kika shiga.
Ko wankan ma, make it stylish & sexy. How?
Ki kama bakin zanin duka biyu, ki daura a kijiki ki kulle, yanda zai zauna das a kirjinki yayi kuma lebatu wic looks very sexy.😃

3) Karki yarda ki tauna kashi a gaban miji.
Domin taunar kashi da shan rake kan canza yanayin mutum.
In har kina so kici kashin bari sai bakwa tare.

4) Idan ke maici ce sosai, karki bari miji ya ganki da tulin abinci a gabanki.
Yi kokari kici rabi kafin ya dawo don kinga in zaki kara kadan zaki diba.😃

5) Don Allah karki gyatsa ko tusa a gaban miji.
I beg you.

6) Karki sakace ko kaki pls.

7) Karki kuskura kiyi soshe soshe domin Bera ce kawai take wannan halin.
Allah kiyashe mu.😃

8) Karki yi karya a gaban sa.

9) Karki zagi, karki kuskura ko da kuwa an bata miki.
Musamman Ashar.
Karki ki yarda.

10) Kar ki kawo masa gulma domin zaki zubar da kimar ki a idonsa.

11) Karki yarda ya ganki da kaushi don Allah... Allah yasa mu dace da fatan zamu gyara rayuwar aure ba abin wasa bane

Copied
Babangida Ibb

SAKO ZUWA GA MAZINATA


ZUWA GA MAZINATA ::YADDA KAYI
HAKA ZA'AYI A NAKA.

Abin mamaki sai kaga mutum
musulmi ya mayar da yin zina babbar
Sana'arsa baya jin kunyar Allah balle
mutanen da take zaune a cikinsu da
yake kallon suna masa kallon mutum
mai mutunci da kima.

Dawa yawan daga cikin masu lalata
tarbiyyar yara mata bayan iyayensu
sun basu cikakkiyar kulawa da
tarbiyya addinin musulunci sai kaga
suna son su kuma su kare yayansu
da kannensu wai kada wani yayi zina
dasu!? wannan ai shine hotiho!.
Wallahi Idan kayi zina da yar wani to
ka tabbatar ko aljanu ka sanya suna
gadinta to sai anzo har cikin falon
gidanka yadda kake hutawa ayi zina
da yarka ta cikinka ko kanwarka.

Sannan Idan kana da hankali ai ya
kamata kayi tunanin wacce zakayi
zina da ita kanwar wani ce, yayar
wani ce, yar wani ce , matar wani ce,
kuma uwar wani ce fa?.
yanzu kana so ayi zina da matarka?
kana so ayi zina da yarka?
kana son ayi zina da uwaka?
kana son ayi zina da yayarka ko
kanwarka?

Tabbas na San ko shakka babu
amsarka zata zama baka so ayi
dasu !, tunda hakane to kai me yasa
zaka je ka lalata tarbiyyar da sukayi
mata?
lokacin da za kayi zina da yarinya sai
ka cire mata Riga , danuwana ka tuna
cewa mahaifinta ne ya saya mata
don kare mata mutuncinta amma kai
kuma sai ka bude mata saboda
rashin imani?.

Idan ka zama mazinaci to ka lalata
zuriyarka gaba daya domin kuwa
Annabi saw ya tabbatara mana da
cewa ana gadon zina daga wajen
mahaifi ko mahaifiya kaga kenan dole
acikin yayanka a samu mazinaci ko
mazinaciya ko baka so kuwa kuma
komai tsarin daka bayar kuwa.
Sannan ka gane zina bata buya ko
Ba a garinku kakayi ba indai kai
mazinaci ne wallahi sai Allah ya tona
maka asiri kowa ya gane halinka.

Ni Sirajoa Isah Yunusa ina rokon
Allah da dukkanin sunayensa
kyawawa ya karemu daga fada cikin
wannan musifar gaba dayan wadanda
suka shiga cikinta kuma manya da
yara Ubangiji idan masu shiryuwane
Ka shiryesu Idan Ba masu shiryuwa
bane Allah ka nisanta su daga
garemu da yayanmu da kannenmu da
matanmu kamar yadda ka nisanta
gabas da yammma.