Sunday, December 29, 2019

YADDA ZAKI MALAKE MIJINKI



YADDA ZAKI MALAKE MIJINKI
1. Ki riqa yi masa halin mata, wato irinsu
kisisina, shagwaba dss, don namiji baya son
mai halin maza ta zama matarsa.
2. Ki zamo mai iya kwalliya. Idan kin kasance
mai zaman gida ce to kici ado ko da kuwa
baza ki fita ko zuwa ko ina ba.
3. Kada ki fara lissafowa mijinki matsalolinki
ko na gida a lokacin da ya shigo, ki barshi ya
huta tukuna ya samu nutsuwa.
4. Ki zamo mai kirki, ladabi da biyayya ga
Mahaifiyar mijinki kamar yadda zaki so
shima ya zamo kamar haka ga mahaifiyarki.
5. Ki dinga qarawa mijinki qarfin gwiwa
akan abinda kika ga alamar yana nema ya
karaya, hakan zai sa ya gwarzo a cikin maza.
6. Ki dinga fadawa mijinki cewa kina sonshi
sau dayawa, dayawa dayawa,
Aisha ﺭﺿﺎﻟﻠﻪ
ﻋﻨﻬﺎ tace Annabin tsira SAW ya kasance yana
tambayarta qarfin soyayyarta gareshi, sai
tace mishi kamar ‘zarge’ (wato dauri ko kulli
wanta bazai kwance ba), sai ya sake
tambayarta ‘yaya zargen yake’? Kuma ya
kasance yana cewa da ita Allah ya saka miki
da alkhairi Aisha, ina farin ciki da jin dadi
dake fiye da yadda kike farin ciki dani!
7. Ki dinga yawan sada zumunci ga mutanen
gidansu (kamar ziyartarsu, kiransu a waya
dss).
8. Ki dinga bashi wani dan qaramin aiki a
gida; kuma idan yayi aikin sai ki gode masa.
Hakan zai sa ya qara dagewa.
9. Ki dinga qarfafa masa zuciya wajen yin
aikin alheri
10. Idan yana cikin damuwa ki dan bashi
lokaci, da yardar Allah sai kiga ya dawo dai
dai.
11. Ki dinga yi masa godiya akan sama miki
abinci da muhalli da yake yi, abune mai
girma!
12. Ki tuna cewa mijinki ma yana da
damuwa da farin ciki, saboda haka ki dinga
tunawa dashi wajen yanke hukunci.
13. Idan mijinki ya nuna damuwa akan dan
qaramin abu da kika yi masa to sai ki bashi
haquri kuma ki dena.
14. Kiyi dukkan abubuwan da aka lissafo
saboda Allah, sai kiga Allah ya sa miki
albarka a cikin duk abinda kike yi.
Allah ya kawo mana albarka da yalwar arziqi
da ta ‘ya’ya a cikin Rayuwar Aure!
'Yan MATA SAMARI ALLAH YA AURAR DAMU GA ABOKANAN ZAMA NA GARI.

No comments:

Post a Comment