Sunday, December 29, 2019

IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA



IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA
Idan duniya tazo Qarshe za'ayi wani dare mai tsawo wanda saboda tsananin duhunsa tsoro zai kama mutane sai su fita zuwa Masallatai suna ta addu'a suna rokon afuwa awajen Allah..
Chan za suga alamar ketowar alfijir, rana zata fito amma ta mafa'darta (wato ta yamma).
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!.
Wannan chanjin yanayin da aka samu shine babbar alamar dake bambanta tsakanin Qarewar rayuwar duniya da kuma ainahin tsayuwar nan ta tashin Alqiyamah.
Da zarar rana ta fito daga mafa'darta (wato yamma) nan take za'a ji kira daga wata murya mai Qarfi..
Tana sabar da mutane cewa "AN RUFE QOFAR TUBA!". Daga lokcin nedukkan wata sha'awa zata fiche daga dukkan zukata, Kuma nadama zata yawaita..
Domin kuwa tuba ba zatayi amfani ga masu yinta ba.. Imani ba zai yi amfani ba, sai ga wadanda suke dashi tuntuni..
Abubuwan dake rike da duniyar dama su hudu ne : - ALQUR'ANI. - KA'ABAH. - MUSULUNCI. - MUMINAI. -
Za'a wayi gari aga Alqur'anai baki daya sun zama farar takarda babu rubutu ko daya.. -
Wani Babban Kafiri zai zo ya rushe Ka'abah (ZUS SAWEEQATAINI) Kuma zai wawashe kayan alatun dake cikinta.. (SUBHANALLAH).
Haka Annabi (saww) ya fa'di sunansa. - Za'a yi wata iska mai dadi wacce zata zama dalilin ficewar rayukan dukkan Muminai..
Su koma zuwa ga rahamar Ubangijinsu. - Za'a wayi gari babu sauran Musulmi ko Muminai aduniya baki daya.
Babu sauran mai cewa "ALLAH! ALLAH!!". - Za'a yi Qarni guda (100 yrs) wanda acikinta babu sauran 'dan halal.. Duk sai Mazinata da 'Ya'yan Zina. Zasu rika yin zina akan layi da bakin tituna.. .
Cikinsu babu wanda yasan Allah balle ya bauta masa.
Sune mafiya sharrin halittu abayan Qasa. Kuma akansu ne Alqiyamah zata tashi.. HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKEEL!!
Ya Allah ka kyautata Qarshenmu kasa mu cika da imani Ameen

No comments:

Post a Comment