Sunday, December 29, 2019

BABBAR MAGANA:



BABBAR MAGANA:
Ranar Lahira Allah yana cewa:
(Ya ku wadanda suka yi imani, ku kiyaye dokokin Allah, kowane mai rai ya dubi abin da ya aikata domin gobe (lahira)…) [Al-Hashri, aya ta 18].
1. Mutuwa ba ita ce karshe ba. Mutuwa mafarin wata rayuwa ce mai tsawon gaske, mai ciki da dadi ko wahala, mai kunshe da farin ciki ko bakin ciki. Duk mai kokwanto game da rayuwar lahira mahaukaci ne ba mai hankali ba.
2. Rayuwarmu a nan duniya tana cike da zalunci da ta'addanci da rashin gaskiya da miyagun ayyuka. An mayar da karya ita ce mafita, yaudara kuma ita ce wayo munafurci kuma ya zamawayewa.
3. A rayuwarmu a yau muna ganin ana hukunta marar laifi a kyale masu laifuka, ana kuma wulakanta mai mutunci sannan a karrama fitsararre. Don haka idan har mun yarda da cewa Allah adalin Sarki ne, to babu makawa dole ne mu yi imani da samuwar wata rayuwa bayan wannan ta duniya da muke ciki, watau rayuwa wadda a cikinta ne Allah zai mayar wa kowane mai hakki hakkinsa, ya hukunta duk wani mai laifi gwargwadon laifinsa. Duk wani mai hankali da ya san ya kamata dole ne ya yarda da haka.
4. Yarda da lahira da imani da sakamakon cikinta ne kadai zai hana wa dan'adam zaluntar dan'uwansa, zai kuma kara wa mutumin kirki kwarin gwiwar aikata ayyukan alheri,domin yana da tabbacin cewa zai ga kyakkyawan sakamakon aikinsa.
5. Ashe bai kyautu mu ci gaba da tunatar da junanmu wannan babbar magana ba

FALALAR RAKA'ATAYIL FAJRI



FALALAR RAKA'ATAYIL FAJRI
*******************************
Raka'atayil Fajri : Sune raka'o'in nan guda biyu na nafila wadanda ake yi bayan Hudowar Alfijir, kafin sallar Asubahi.
Wannan sallar tana da inganci sosai. Domin Annabi (saww) ya bata muhimmanci. Ya kasance yana yinta aduk halin da yake ciki. Koda awajen tafiya, ko azaman gida.
Malamai sun ce ana karanta Fatiha ne da Qul Ya ayyuhal Kafirun, da kuma fatiha da Qul Huwal-Lahu acikinta. KUMA ana yinta ne aboye. (wato yana yin karatunta a sirrance).
Daga cikin falalarta, Sayyiduna Abdullahi bn Umar (rta) ya ruwaito cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) cewa :
"Ya Rasulallahi ina so ka nuna min wani aiki wanda Allah zai amfanar Dani saboda shi".
Sai Annabi (saww) yace masa "KA KULA DA RAKA'ATAYIL FAJRI DOMIN ACIKINTA AKWAI FIFIKO (WATO FALALA)".
(Tabaraniy ne ya ruwaitoshi).
Acikin wata ruwayar kuma Abdullahi bn Umar (ra) yace "Naji Manzon Allah (saww) yana cewa :
"KAR KU BAR YIN RAKA'O'IN NAN GUDA BIYU WADANDA AKEYI KAFIN SALLAR ASUBA. DOMIN ACIKINSU AKWAI ABABEN KWADAYI".
Domin cikar fa'idah ma, ga wani Sahihin hadisin wanda Imamu Muslim ya ruwaito daga Nana A'ishah (ra) ita kuma daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"RAKA'O'I BIYUN ALFIJIR, SUN FI DUNIYA DA ABIN CIKINTA".
Don haka 'yan uwa bai kamata mu rika barin wannan garabasar tana wucemu ba.
Da yawan Matasa Wasu basu yinta. Dama basu kwanciya da wuri, shi yasa suke makara. Kuma da zarar sun tashi sai su sallaci Asubah, ita kuma su kyaleka.
To lallai rashin yin RAKA'ATAYIL FAJRI ba Qaramar Asara bace agareka ya kai Musulmi!
Wannan asarar tafi asarar Biliyoyin Nairori. Domin kuwa Annabi (saww) yace TAFI DUNIYA DA ABIN CIKINTA. Don haka idan baka yita ba, kamar kayi asarar dukiyar dake cikin duniyar nan ne. Ko kuma fiye da haka.
Na san yanzu wani zai ce "Shin zan iya yinta koda bayan Sallar Asubah ne?".
AMSA : A'a. Ana yinta ne kafin sallar Asubah. Domin bai halatta kayi sallar nafila bayan kayi ta Asubahi ba. Har sai bayan fitowar rana.
Hujjah anan ita ce Sahihin hadisin da Imamul Bukhariy da Muslim suka ruwaito daga Abu Sa'eed Alkhudriy (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"BABU SALLAH (NAFILAH) BAYAN SALLAR LA'ASAR HAR SAI RANA TA FADI. KUMA BABU SALLAH BAYAN SALLAR ASUBAH HAR SAI RANA TA BULLO".
Wani Sahabi mai suna Amru bn Abisata (ra) yace "Ya Rasulallahi bani labari mana game da sallah".
Sai yace masa "KA SALLACI ASUBAH SANNAN KA JANYE DAGA YIN SALLAH HAR SAI RANA TA FITO TAYI SAMA.....".
Imamu Ahmad da Muslim ne suka ruwaitoshi).
Mafiya yawan Jamhurin Malamai suna ganin halaccin yin ramukon sallah akowanne lokaci, koda bayan Sallar Asubah din ne. Amma banda nafila.
Saboda hadisin da Imamul Bukhariy da Muslim suka ruwaito daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"DUK WANDA YA MANTA DA WATA SALLAH (TA FARILLAH KENAN) TO YA SALLACETA IDAN YA TUNA".
Amma yin nafila bayan Sallar Asubah, mafiya yawan Sahabbai duk sun karhanta yin haka. Kamar Irin su Sayyiduna Aliyu Bn Abi Talib. Da Ibnu Mas'ud da Zaidu bn Thabit da Abu Hurairah da Ibnu Umara (Allah shi yarda dasu baki dayansu).
Sayyiduna Umar kuwa, ya kasance yakan bugi mutum idan ya ganshi yana yin nafila a irin wadannan lokutan.
Hakanan Sayyiduna Khalid bn Waleed (ra) Shima yakan bugi masu yin hakan. (Wato masu yin nafila alokutan da aka hana).
Duk da cewa akwai Maluman da suka halatta yinta bayan an sallaci Asubah, wai saboda Hadisin wani mutum wanda ya tashi bayan Sallar Asubah yana yinta amma Annabi (saww) bai ce masa komai ba. To amma gaskiya hujjarsu bata kai wannan din Qarfi ba. ta kowacce fuska.
Saboda wannan haka Annabi (saww) yake yi, Haka Khalifofinsa gaba daya suke yi. Hakanan duk manyan Sahabbansa wadanda aka riko sunnah daga garesu duk suna yinta ne kafin sallar Asubahi (Ba bayanta ba) Haka kuma, dukkan Maluman Mazahib din nan guda hudu.
Anan zan tsaya, sai wani lokacin kuma in sha Allahu. Da fatan Allah shi amfanemu da abinda muka karanta.
An gabatar da karatun a Zauren Fiqhu -3 (28-02-2016).
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP. (07064213990).

DALILAI 11 DAKE JAWO ARZIKI



DALILAI 11 DAKE JAWO ARZIKI. DAGA KUR'ANI DA HADIS.
1 Ilimi da kwazon aiki da shi.
2 Dogoro ga Allah ta'ala kawai. suratul dalaki 3
3 Istigifari suratul nuh. 10-12 4 Tuba na gaskiya suratul hud 3
5 Tsoton Allah S.W.T. suratul.A'Araf 96
6 Anbaton Allah a Zuci da baki da gabbai. suratul daha 124
7 Ciyarwa da taimakon na kasa. suratul saba'I. 39
8 Sada zumunta. Buhari, Muslum, Nasaiy, Ibn Majah, Al Imam Ahmad da Abu Dauda
9 Addu'a , Allah ina neman tsarinka daga talauci da kafirci.
10 Taimakawa daliban Ilimi. Attirmiziy
11 Godiya ga Allah ta'ala. suratul Ibrahim 7

KUSKUREN DA MATA SUKE AFKAWA YAYIN 'DAUKEWAR JININ HAILA


KUSKUREN DA MATA SUKE AFKAWA YAYIN 'DAUKEWAR JININ HAILA*
_______________
Mafi yawan mata idan jinin al'ada ya 'Dauke musu suna jinkirta wanka da niyar ko jinin zai Qara dawowa.
Wasu sukan Qara kwana 'Daya zuwa biyu bayan haila ya 'Dauke.
Wasu kuma idan suka ga alama guda 'Daya na 'Daukewar jinin, sai suce zasu jinkirta wanka domin su jira zuwan sauran alamomin. Misali: Mace taaga bushewar gaba amma bata ga Farin ruwa ba, wanda ake kiransa da larabci (قصة البيضاء), daga nan sai tace bari ta bari sai farin ruwa yazo sannan tayi wanka ta cigaba da sallah da azumi.
Duka Wannan kuskure ne babba
Abinda yake wajibi shine: Da zarar taga jini ya tsaya ko taga alamomin Daukewar Jinin haila, toh wajibi ne tayi wanka nan take ta cigaba da ibadar ta. Qin yin wanka har lokacin sallah ya wuce babban zunubi ne.
Allaah ya tanadi Azaba mai tsanani ga masu wasa da sallah.
Allaah yace:-
" ﻓَﻮَﻳْﻞٌ ﻟِﻠْﻤُﺼَﻠِّﻴﻦَ ‏(4 ‏) ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻫُﻢْ ﻋَﻦْ ﺻَﻠَﺎﺗِﻬِﻢْ ﺳَﺎﻫُﻮﻥَ "
{ﺍﻟﻤﺎﻋﻮﻥ : 5-4 }
Allaah ya qara da cewa:-
" ﻓَﺨَﻠَﻒَ ﻣِﻦْ ﺑَﻌْﺪِﻫِﻢْ ﺧَﻠْﻒٌ ﺃَﺿَﺎﻋُﻮﺍ ﺍﻟﺼَّﻠَﺎﺓَ ﻭَﺍﺗَّﺒَﻌُﻮﺍ ﺍﻟﺸَّﻬَﻮَﺍﺕِ ﻓَﺴَﻮْﻑَ ﻳَﻠْﻘَﻮْﻥَ ﻏَﻴًّﺎ "
{ﻣﺮﻳﻢ : 59 }
...... Da ayoyi masu yawa cikin al-Qur'ani.
daga lokacin da jini ya 'Dauke, ibada ya wajaba ga mace.
idan mace ta jinkirta sallah toh sai ta rama su bayan tayi wanka, sannan tayi istigfarin jinkirin sallah
*_Idan kin karanta kiyi Qoqarin turawa yar uwarki musulma zaki samu lada in shaa Allaah_______

FA'IDODIN DA SUKE CIKIN YIN AURE




FA'IDODIN DA SUKE CIKIN YIN AURE
*************************************
Fa'idodin da suke cikin aure ba zasu
Kididdigu ba. Amma ga wasu ka'dan
daga ciki zamu lissafo kamar haka:
1. Yin aure biyayya ne ga Umurnin
Allah da Manzonsa.
2. Yin aure yana sanya Manzon Allah
(saww) farin ciki aranar lahira. Yace :
"Kuyi aure ku hayayyafa. Domin ni
zanyi ma sauran al'ummomi alfahari
daku aranar Alkiyamah".
3. Ta dalilin aure zaka samu wanda
Zai fito ta jikinka, har ya girma yana
Kalmar Shahada!! "LA ILAHA ILLAL
LAHU MUHAMMADUR RASULALLAHI".
4. Ta dalilin aure ne zaka samu
Zuriyar da zasu yi maka addu'a
bayan rasuwarka. Wannan yana daga
cikin ayyukan da ladansu ba zai
yanke ba har abada.
5. Yin aure ya kan zama dalilin
runtsewar idanun mutum daga kalle
kallen Haramun, sannan ya kare masa
al'aurarsa daga Zina.
6. Ta dalilin aure ne zaka samu
damar taimaka ma 'Yar uwarka
Musulma, ka aureta, ka Kiyayeta
kenan daga Zina.
7. Ta dalilin aure ne zaka samu cikar
addininka, da ninkawar ladanka fiye
da wanda bashu da aure.
8. Ta dalilin aure ne zaka samu ladan
ciyarwa da Matarka, da daukar
nauyinta, da ladan samar mata da
Mazaunin da zata rayu.
9. Ta dalilin aure ne zaka samu
damar Qara yawan Musulman duniya
ta hanyar haihuwar da zaka samu.
10. Ta dalilin aure ne zaka samu
damar Karkatar da himmarka daga
kan neman biyan bukatarka ta hanyar
haram izuwa ga hanyar halal. Da
kuma samun ladan saduwa da
iyalanka.
11. Zaka samu lada mai girma sosai
idan Har Allah ya azurtaka da 'Ya'ya
mata guda biyu, kumq kayi hakuri
dasu ka kyautata musu, ka kyautata
tarbiyyarsu, Su zasu zama
Garkuwarka daga shiga wuta.
12. Idan ka har 'Ya'yanka guda biyu
suka rasu, kuma kayi hakuri, to Allah
zai shigar dakai Aljannah saboda
wannan.
13. Ta dalilin aure zaka samu
Qaruwar mutuncinka da darajarka
acikin al'ummah. Ka shiga sahun
mutanen da zasu iya jagorantar
lamuran rayuwar al'ummah.
14. Ta dalilin aure ne zaka Samu
Taimakon Allah cikin al'amarinka.
Kamar yadda Manzon Allah (saww)
yake cewa: "
MUTUM UKU, HAKKI NE
AKAN ALLAH YA TAIMAKESU. 1.
WANDA ZAI YU AURE DON NUFIN
KAME MUTUNCINSA. 2. BAWA
WANDA YAKE NEMAN 'YANCINSA
SABODA YA SAMU DAIDAITUWA
(ACIKIN ADDINI) 3. MUJAHIDI (MAI
YAKIN DAUKAKA ADDININ ALLAH

MARRIAGE TO MORETHAN ONE WIFE



MARRIAGE TO MORETHAN ONE WIFE
------------
*Quran' chapter 4 verse 3 (suratu-nisai)*
.........فانكحواماطاب لكم من النساء مثن وثلث وربع........
*.............marry 2, or 3, or 4. But if u are are afraid of justice amongst ur wives,,,then marry one.*
--------------
*JUSTICE AMONG WIVES*
*Qur'an chapter 4 verse 128*
ولن تستطيعواان تتعدلوا بين النساءولوحرصتم فلاتميلواكل الميل...........
*U will not be able to do justice (( interms of LOVE//FEELINGS ))among ur wives, even if u strive to do so. But do not turn completely (openly) for only one of them.............*
++++++++++
*Justice in this verse is not interms of LOVE but interms of shelter,feeding, dresses,children etc etc etc.*
+++++++++
*DID U EVER THINK OF THESE?*
*1. Birth rate statistics shows dat 65% of birth are girls and only 35% are boys.*
*2. Did u ever go to schools? ( primary,secondary,tertiary ),,the ratio of male : female is approximately 35:65*
*3. Death rate statistics shows dat male 60%, female 40%. Accident claims more male than female due to struggle for survival. Plus other ways.*
*4. Did u ever compare the physical outlook of a man of 45 years with a female of 45 years? Who among them look seriously younger?*
+++++++++
*I remember hadith of d prophet Muhammad SAW*
لايومن اهدكم حتى يحب لاخه ما يحب النغسه
*U are not a believer, EXCEPT u love for ur fellow what u love for Urself*
++++++++
*DISTURBING QUESTIONS*
*1. What will happen to the remaining population of females, if every man should marry only one wife?*
*2. If u give birth to 5 female children, and u also have very plenty sisters who are yet to marry. WHO WILL MARRY them.*
*3. If a woman got married to a man at d age say 20-25. And d husband eventually died 5years after their marriage. Is that how d woman will die without remarriage?*
😳😳😳😳
😭😭😭😭
*My brother//sister inslam,,, we should fear Allah and love for others what we love for ourselves.*
+++++++
*U can not stick to only one wife when u are blessed to some extent to marry 2, or 3, or 4,,, OR WOMEN THAT ARE TROUBLING THIER HUSBAND NOT TO MARRY ANOTHER WIFE,,,and yet u expect ur daughters to get married with ease.*

MACE MAI WUYAR SAMU A YAU



MACE MAI WUYAR SAMU A YAU
__________________________________
Ya kamata mu sani cewa mace daya ce a duniya take da wuyar samu, amma idan ka samu irinta, kada ka kuskura ka rabu da ita. Ya halatta ka auri mace fiye da daya, amma ka sani, mace daya ce kawai, ta ke yin tasiri a rayuwa, wacce ranka kullum zai kasance a kanta.
Babbar tambaya a nan ita ce, wacece wannan dayar? Ita ce wadda duk da namiji yake muradin samu a rayuwarsa, Ita ce wadda ke koyi da rayuwar shugabar matan duniya kuma diya ga Rasulallahi (SAW), wato Nana Fatima (Allah Ya kara mata yarda).
Haka kuma ita ce wadda kowace mace take fata ta zama.
Ga siffofinta guda goma, kamar.
haka:
1. Matar da ta yarda ita mace ce, don haka ta tanadi duk abin da ake bukata a wajan mace.
2. Mace mai hikma da azanci, wacce ta karanci mijinta da kyau, kuma take kaucewa duk abin da
zai haddasa matsala a tsakaninsu.
3. Mace mai taushin hali da nutsuwa, wacce miji yake jin nutsuwa, idan yana tare da ita.
4. Mace da kudi bai dame ta ba, ita mijinta kawai take so, ko da akwai ko babu.
5. Mace mai hakuri da juriya, babu gunaguni, babu mita, da kai kara ga iyaye ko kawaye.
6. Macen da ta dauki kanta likita, mijinta mara lafiya, domin ya sami kulawa, ta musamman da.
riritawa.
7. Mace mai saurin daukar ishara, tana gane shiru da magana, da motsi da yanayin shigowa da
fita, samu da rashi da kuma yanayin da ake ciki a duniya ko a gari.
8. Mace mai sakakkiyar zuciya, mara kulli da ramuwa.
9. Mace mai karawa miji kuzari da karfin hali, a kan kyawawan manufofinsa.
10. Mace mai rikon amanar aure, da soyayya ga mijinta kawai.
Fatanmu ubangiji yasa mudace da mata na Kwarai.

ABU-BUWAN DA SUKE HADDASA WARIN BAKI



★ABU-BUWAN DA SUKE HADDASA WARIN BAKI★
★Halitosis★ Mouth odour or bad breath★
Shi warin baki yana haddasuwa ne ta hanyoyi gida biyu..!
1★ Local factors
2★ Systemic factors.
Local factors ;- sune wadanda ke faruwa ta sanadin Abubuwa kamar haka;
1_Rashin tsaftar baki... (Rashin yin brush,ko rashin yin Sa dakyau) Shine zakuga haqora sun chanja colour ,da zarar an bude baki sai waari..
2_Kogon haquri.. (Wato wadanda sukeda da kogo a haqoransu)
3_Cin Tafarnuwa... (Amfani da ita,dayawa,Yana kawo warin baki)
4_Ka yan Qamshi ,wadanda ake sawa a Abinci... (Irinsu curry ,tyme da sauransu)
5_Albasa (itama cinta da yawa,yana kawo warin baaki)
6_Dadewa ba,ayi magana ba shima yana kawo warin baki(idan ka bude baki zakaji bakin yana hamami na wari amma ba sosaiba)
7_Tashi da sassafe idan ka bude bakinka zakaji yana hamami (early morning breath)
Wadannan sune local factors dasuke kawo warin baki za,a iya maagance wannan matsalar,gurin Rage Cin Albasa,tafarnuwa,spices, Saikuma a rinqa yin brush dakyau ,so biyu a yini,da safe bayan Karin kumallo,ayi brush,da daddare kafin akwanta barcin dare...
SAI ziyartar Dental clinic, duk bayan wata shida..domin a wanke maka haqoranka...
NAN GABA INSHA ALLAH ZAN KAWO SYSTEMIC FACTORS DAKUMA YANDA ZA,A MAGANCE SU...
★Ni Safeeyyah Suleiman Umar
Nake cewa mu wuni lafiya

YADDA ZAKI MALAKE MIJINKI



YADDA ZAKI MALAKE MIJINKI
1. Ki riqa yi masa halin mata, wato irinsu
kisisina, shagwaba dss, don namiji baya son
mai halin maza ta zama matarsa.
2. Ki zamo mai iya kwalliya. Idan kin kasance
mai zaman gida ce to kici ado ko da kuwa
baza ki fita ko zuwa ko ina ba.
3. Kada ki fara lissafowa mijinki matsalolinki
ko na gida a lokacin da ya shigo, ki barshi ya
huta tukuna ya samu nutsuwa.
4. Ki zamo mai kirki, ladabi da biyayya ga
Mahaifiyar mijinki kamar yadda zaki so
shima ya zamo kamar haka ga mahaifiyarki.
5. Ki dinga qarawa mijinki qarfin gwiwa
akan abinda kika ga alamar yana nema ya
karaya, hakan zai sa ya gwarzo a cikin maza.
6. Ki dinga fadawa mijinki cewa kina sonshi
sau dayawa, dayawa dayawa,
Aisha ﺭﺿﺎﻟﻠﻪ
ﻋﻨﻬﺎ tace Annabin tsira SAW ya kasance yana
tambayarta qarfin soyayyarta gareshi, sai
tace mishi kamar ‘zarge’ (wato dauri ko kulli
wanta bazai kwance ba), sai ya sake
tambayarta ‘yaya zargen yake’? Kuma ya
kasance yana cewa da ita Allah ya saka miki
da alkhairi Aisha, ina farin ciki da jin dadi
dake fiye da yadda kike farin ciki dani!
7. Ki dinga yawan sada zumunci ga mutanen
gidansu (kamar ziyartarsu, kiransu a waya
dss).
8. Ki dinga bashi wani dan qaramin aiki a
gida; kuma idan yayi aikin sai ki gode masa.
Hakan zai sa ya qara dagewa.
9. Ki dinga qarfafa masa zuciya wajen yin
aikin alheri
10. Idan yana cikin damuwa ki dan bashi
lokaci, da yardar Allah sai kiga ya dawo dai
dai.
11. Ki dinga yi masa godiya akan sama miki
abinci da muhalli da yake yi, abune mai
girma!
12. Ki tuna cewa mijinki ma yana da
damuwa da farin ciki, saboda haka ki dinga
tunawa dashi wajen yanke hukunci.
13. Idan mijinki ya nuna damuwa akan dan
qaramin abu da kika yi masa to sai ki bashi
haquri kuma ki dena.
14. Kiyi dukkan abubuwan da aka lissafo
saboda Allah, sai kiga Allah ya sa miki
albarka a cikin duk abinda kike yi.
Allah ya kawo mana albarka da yalwar arziqi
da ta ‘ya’ya a cikin Rayuwar Aure!
'Yan MATA SAMARI ALLAH YA AURAR DAMU GA ABOKANAN ZAMA NA GARI.

AQIDAR SHI'AH IMAMIYYA NA KAFIRTA SAHABBAN MANZON ALLAH (S.A.W)**




AQIDAR SHI'AH IMAMIYYA NA KAFIRTA SAHABBAN MANZON ALLAH (S.A.W)**
Wallafar :Muhammad ibn yusuf Alkarofiyyah
Tattarawa + Tsarawa : Jamilu ibrahim sarki..
Rubutawa ; Safeeyyah Suleiman Umar (Ama~natullah)
A dalilin aqidar shi'a na 'karya cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ayyana Sayyiduna Aliyu (R.A) a matsayin halifa a bayansa wai sai sahabbai (R.A) suka sa6a wasiyyar don haka sukace sunyi Ridda.
Wa, iyazubillah .! Kada in ja ka da nisa ka duba littafin #ALKAFI na #KULAINI a cikin kitabul _Raula ..
Mujalladi na takwas (8) shafi na 167 ..
Hadisi mai lamba 341, suka ce Abu ja,afar ya ce "Mutane (watau sahabbai) sun kasance Riddaddu bayan rasuwar Manzon Allah (S.A.W) sai dai mutane uku (3) kawai, sai aka tambayi shi su wane ne mutane ukun sai ya c "#Miqdad_ibn_Aswad da #Abu_zarril_gifari da kums #Salmanul_farisi..
Allahvdarki 'YAN #SHI_AH sai suka manta da sukace mutane uku ne kawai basu yi riddah ba.!
To ya matsayin Aliyu.! Da fatima.! Da Alhassan.! Da Alhussain.! Da 'Dan Abdullah.! Da huzaifa.! Da Bilal.!,
A wancam lokacin Allah ya yarda dasu.??
Da ma 'KARYA Rusash_shiya ce, ka ga ya nuna 'Dimaucewar :#YAN SHI 'AH ...
ALLAH YA SHIRYAR DA MU....
Ameeeen..

YADDA ZA A WANKE QODA



YADDA ZA A WANKE QODA (KIDNEY) CIKIN SAUKI BA TARE DA YIN DIALYSIS A ASIBITI BA!
A nemi Ganyen Yalo🌿 wato (Garden Egg Leaves), Sai a Dan wanke ganyen da Ruwa me kyau Sai a yayyankashi🔪🌿 kanana-kanana, Sai a zuba a tukunya me kyau tare da ruwa me kyau, Sai a dora a kan wuta tsawon mintuna goma 10.
Sai a tace a saisaitashi kaman shayi🍵, idan ya Dan huce Sai a shanye cikin karamin Kofi daya🍵, Bayan an shanye da Dan wasu awowi in aka ji fitsari a yi a fili ta yadda za a ga kalar Fitsarin ya chanza tare da fitar da wasu cututtuka Daga Qoda (Kidney) Zuwa mara.
Me fama da Ciwon Qoda ya jarraba Wannan bayani InshaaAllahu zai dace da waraka da yardar Allah! Me fama da ciwon Qoda yana iya yi kullum sau Biyu a rana har ya dace, me son ya wanke Qodarsa kuma Sai ya dinga yi sau daya a kowacce rana Na tsawon sati daya.
Yah Allah👏🏻 ka bamu Lafiya da zaman lafiya, yi kokarin turawa Contacts da Groups naka domin Baka San adadin rayukan Dubban Al'ummar da zaka ceto ba kuma zaka samu Lada me yawa.

IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA



IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA
Idan duniya tazo Qarshe za'ayi wani dare mai tsawo wanda saboda tsananin duhunsa tsoro zai kama mutane sai su fita zuwa Masallatai suna ta addu'a suna rokon afuwa awajen Allah..
Chan za suga alamar ketowar alfijir, rana zata fito amma ta mafa'darta (wato ta yamma).
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!.
Wannan chanjin yanayin da aka samu shine babbar alamar dake bambanta tsakanin Qarewar rayuwar duniya da kuma ainahin tsayuwar nan ta tashin Alqiyamah.
Da zarar rana ta fito daga mafa'darta (wato yamma) nan take za'a ji kira daga wata murya mai Qarfi..
Tana sabar da mutane cewa "AN RUFE QOFAR TUBA!". Daga lokcin nedukkan wata sha'awa zata fiche daga dukkan zukata, Kuma nadama zata yawaita..
Domin kuwa tuba ba zatayi amfani ga masu yinta ba.. Imani ba zai yi amfani ba, sai ga wadanda suke dashi tuntuni..
Abubuwan dake rike da duniyar dama su hudu ne : - ALQUR'ANI. - KA'ABAH. - MUSULUNCI. - MUMINAI. -
Za'a wayi gari aga Alqur'anai baki daya sun zama farar takarda babu rubutu ko daya.. -
Wani Babban Kafiri zai zo ya rushe Ka'abah (ZUS SAWEEQATAINI) Kuma zai wawashe kayan alatun dake cikinta.. (SUBHANALLAH).
Haka Annabi (saww) ya fa'di sunansa. - Za'a yi wata iska mai dadi wacce zata zama dalilin ficewar rayukan dukkan Muminai..
Su koma zuwa ga rahamar Ubangijinsu. - Za'a wayi gari babu sauran Musulmi ko Muminai aduniya baki daya.
Babu sauran mai cewa "ALLAH! ALLAH!!". - Za'a yi Qarni guda (100 yrs) wanda acikinta babu sauran 'dan halal.. Duk sai Mazinata da 'Ya'yan Zina. Zasu rika yin zina akan layi da bakin tituna.. .
Cikinsu babu wanda yasan Allah balle ya bauta masa.
Sune mafiya sharrin halittu abayan Qasa. Kuma akansu ne Alqiyamah zata tashi.. HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKEEL!!
Ya Allah ka kyautata Qarshenmu kasa mu cika da imani Ameen

DOMIN TABBATAR DA LAFIYAR BAKINMU



DOMIN TABBATAR DA LAFIYAR BaaKINMU★★★
CIKON ABUBBUWAN DA SUKE HADDASA WARIN BAKI..
___________________________________________________________
Kwankin baya nayi bayani akan causes of bad breath,or bad odour...
Wanda nace sunkasu zuwa gida biyu..
Local factors
Systemic factors....
Nayi bayanin local factors kuma nafadi hanyoyin da inshaa Allah idan akabi za,a maagance su da izinin Allah...
Yanzu zamuyi bayani akan systemic factors...
★SYSTEMIC FACTORS★
Su wadannan systemic factors din sune ake samu a system din mutum..
Wato acikin jikin mutum ake samunsu...sai su HADDASA warin baki...ko hamami....
Sune kamar haka..
1_ Akwai Diabetes.. Wato ciwon sugar dayane daga cikin cutukan da suke HADDASA warin baki..
Mussamman idan mutum baaya shan maganin ciwon sugar kuma bai kula da tsaftar baakinsa.. Zai kamuwa da waarinbaki...
2_ Hepatitis.. Ciwon hanta.. Shima kan iya HADDASA warin baki...Amma idan ana shan magani ana kulada tsaftar haqora ..Angujewa kamuwa da cutar warin baki..
3_Pregnancy.. Juuna biyu shima yana HADDASA warin baki..
Idan Ana kula da haqora,za,a gujewa kamuwa da warin baki..
Musamman bayan Anhaihu shikenan..
4_Drugs...kwayoyin magana ,suka suddasa warin baki..
Misali Antibiotics drugs ,amma dazarar Angama shan magungunan shikenan Anrabu da warin baki..
5_Menstrural pain... Ciwon Al'ada na mata.. Shima yana HADDASA warin baki..Dazararr ankammala shikenan anrabuda warin bakin...
5_Blockage of the cynosis.. Mura ma tana HADDASA warin bai lokacin da kafafen hanci suka too she... ,idan aka shan maganin mura aka warke shikenan anrabu da warin baki ko hamami....
Kasance mai tsafatace HAQORANMU akowane lokaci..
Sai biyu ayini...kafin akwanta barcin dare dakuma bayan antashi barcinsafe bayan breakfast..
Ziyartar Dental clinic duk bayan wata shida domin tsaftace maka haqoranka..
Idan kanada wata matsala abakinka maza garzaya Dental clinic. ,domin magance matsalar cikin sauki...
★AKULLUM LAFIYAR BAAKINMU DA HAQORANMU ITACE JARINMU★
Kuci gaba da bibiyar rubutuna domin jin saabon topic...
Ni Safeeyyah Suleiman Umar
Nakecewa Mu kwana lafiya
12/9/2018

TO ENSURE ORAL HYGIENE





TO ENSURE ORAL HYGIENE
Shin me yasa wani lokacin zamuga muna 'koqarin goge haqoran mu Amma ba daama mu bude bakin mu sai wari????
Halitosis (Bad breath or bad odour) Wata cuta wadda take samuwa sanadin Rashin kula tsafatar bakinmu.
Shin kasan cewa acikin bakin mu akwai thousands of bacteria.... Wadanda suke rayuwa acikin bakinmu...??
Su wadannan bacteria da suke cikin bakin mu Allah ya halicce sune acikin bakinmu kamar yanda acikin cikinmu Akwai bacteria da suke rayuwa...
Abunda yake faruwa kaji bakin Na waari Alhalin mutum yana qoqarin goge haqoransa,shine ..
Idan har ka goge haqoran ka baka goge harshenka ba ,To Aikin banza ne domin harshenka shine Mafi daukan datti... Ka kasance bayan ka goge haqoran ka to ka goge harshenka daga qarshe..!
Warin baki wasu naasu yana faruwane sanadin WASU cutuka dasukeda su acikin cikin su, bakinsu zai iya Saina wari ,bayan magance matsalan dayake damunsu acikinsu...
Xasu iya rage matsalan warin bakinsu,ta hangar
Amfani da aswaki....
Sai kuma amfani da mouth fresher,
Ko Amfani da kanumfari...
Warin baki (Halitosis) ,Wasu yana faruwane sanadin caries (kogon Haqori) idan haqorinka yayi kogo wannan ragowar Abincin dayake shiga batare da Anacirewa ba gurin zai rube yadinga waari,kaji idan mutum yabude baki kamar ka suuuu~meeeee~ sabda waaa~riyyy...! pls.Akula.!!!
Idan kaji haqorinka ya faara kanaci Abinci naa maqalewa to maaza garzaya Dental clinic Domin acike maka raamin haqorin..
Amma idan kabari Ramon haqorin yaaci gaba har ya ta6o jijiyar haqorin.. to sai dai Acire haqorin.. Ko kuma ayi maka RCT (Root canal treatment) wato a kwakule jijiyoyin haqorin.. A kashe haqorin batare da Ancireba sai acike shi.. Yazama haqorin bashida rai kenan...
Idan kuma mutum yanaso Amasa Haqorin roba to (Denture) za,ayimasa...
Wadannan sune kadan daga cikin Abinda ke kawo waarin baki..(Halitosis)
Ka. Kasance Mai yawan yin Aswaki.. Sunnah CE ta Annabi (S.A.W) wallahi idan ka kasance kanayi bakai baa warin baki kuma bakai ba matsalar haqora ,HAQORANMU zasu kasan CE fararee Qar~Qar..
Shin kunsan kuwa waareen baki Sanadinsa Auratayya Sunsha mutuwa..
Wani Auranma sati biyu dayinsa yaa mutu sanadin Bad oral hygiene..
Mata da Maza Akula da wannan...
Miji kar ka kuskura Mangoge bakin iyalinka yaqare,dazarar kaga ya kusa qarewa yi kokari ka siyo wani domin gudun kamuwa da warinbaki...
Samari Akula tsaftar haqora..taam!!!
'Yan mata a kulaa fa taaam.!!
Iyaye mata Akula da tsaftar haqoran yaranku...
Taaku har kullum.
Safeeyyah Suleiman Umar (Dentist)
Ina barar Addu'a 'yana uwa
Kubiyoni domin jin sabon topic.
*