Thursday, April 16, 2020

TARBIYYAR YARA



TARBIYYAR YARA A MUSULUNCI. //1
TARBIYYA hakkine da Allah (SWT) ya wajabtawa Iyaye suyi ga 'ya'yansu, kamar yadda ya wajabtawa 'ya'ya yin biyayya ga iyayensu.
Kamar yadda muka sani, 'ya'ya kyautace (Ni'imace) daga Allah da yake bayar da ita ga wanda yaga dama, kuma Amanace da Allah ya dankata a hannun iyaye. Sabida haka Iyayen da suka kyautata wajen tarbiyyantar 'ya'yansu da ladabtar dasu bisa koyarwar Musulunci, to sun sauke wannan amanar, Wadanda kuma suka yi sakaci kuma suka takaita wajen yi musu tarbiyya to sun tozarta wannan Amanar.
Allah Ta'ala yace: " Ya ku wadanda su kayi imani, ku tsare kawunanku da iyalanku daga wuta, wacce mutane da duwatsu ne makamashinta... "
(Tahrim: 6).
Annabi (SAW) yana cewa a wani hadisi:
" Dukkanninku masu kiwone kuma ababan tambayane dangane da kiwon da aka baku, shugaba me kiwone (dangane ga talakawansa) kuma abin tambayane dangane da kiwon da aka bashi, mutum me kiwone dangane ga iyalinsa kuma abin tambayane dangane da kiwon da aka bashi."
Bukhari da Muslim.
Akwai wasu hanyoyi wadanda idan muka bisu zasu taimaka mana da yardar Allah wajen Tarbiyyar 'yayanmu, daga cikinsu akwai:
1. MU ZABAWA 'YA'YANMU UWA TA GARI.
Auren mace tagari muhimmin lamarine dake taimakawa wajen tarbiyyar 'ya'ya, domin uwa ita ce makaranta ta farko da yaro ke daukar darasi a cikinta, kuma halaye da dabi'un uwa suna tasiri matuka ga 'ya'yanta, sabida hakane shari'a ta kwadaitar damu wajen auren mace tagari ma'abociyar addini.
Annabi (SAW) yana cewa: " Ana auren mace sabida abubuwa guda 4; dukiyarta, da kyawunta, da daukakarta, da addininta. ka zabi ma'abociyar addini, sai hannunka yayi albarka."
Bukhari da Muslim.
Abu ne mai muhimmanci ga wanda yake da niyyar yin aure ya dage da addu'a akan Allah ya azurtashi da samun mace tagari, kuma yayi "istikhara" wato neman shawarar (zabin) Allah kafin auren, ya kuma nemi shawarar bayin Allah mutanen kirki, sannan yayi kokari wajen yin bincike akan nagartar yarinyar da kuma iyayenta, ya kuma fawwala al'amuransa zuwa ga Allah SWT.
Sannan kuma ya zama wajibi abi hanyoyin da Shari'a ta tsara wajen neman aure, kuma a nisanci sabawa Allah da sunan murna ko farinciki a yayin aure, wannan zai sa Allah Ta'ala ya sanya Albarka a cikin auren da kuma zuriyar da za a samu ta dalilin wannan auren.
2. ROKON ALLAH YA BAKA ZURRIYYA TA GARI.
Wannan dabi'ace ta Annabawa da Manzanni da bayin Allah salihai. Kamar yadda Allah ya bamu labari a kissar Annabi Zakariyya (AS), yake cewa: " A yayin nan Annabi Zakariyya ya roki Ubangijinsa, yace: ya Ubangiji ka bani kyauta daga gareka ta zuriyya tsarkakakkiya, hakika kai mai amsar addu'ane."
(Ali-Imran: 38)
A wata ayar kuma Allah ya bamu labarin salihan bayinsa, daga cikin siffofinsu suna addu'ar Allah ya basu mata da 'ya'ya nagari, yake cewa:
" Wadannan da suke cewa ya Ubangijinmu ka bamu kyauta daga matayenmu da zuriyyarmu abinda idanuwanmu za suyi sanyi dasu, kuma ka sanyamu mu zama shugabanni ga masu tsoron Allah."
(Al-furqan: 74)
Wannan ya nuna mana muhimmancin addu'a da rokon Allah wajen samun 'ya'ya nagari kasancewar har Annabawan Allah da Salihai sun yi irin wannan addu'ar.
Allah ya bamu ikon yiwa 'ya'yayenmu tarbiyya da ladabdar dasu bisa koyarwar Kur'ani da Sunnah,

Thursday, March 26, 2020

GANIN GASHIN CORONA VIRUS




GASHIN_CORONAVIRUS..
ALHAMDULILLAH
Na kammala dukkanin binciken da zanyi akan wannan GASHIN... Kuma zahiri Naga GASHIN agurare MAban-banta....
A'INA NAGA GASHIN KUMA MAI NE NE SHAIDA.!
Dafarko na Dauko ALQUR'ANI NAH ,na duba bangani ba, Na sake dauko wani ALQUR'ANI NAH Wanda bancika amfani dashi ba....
Ina daukowa Naduba suratul Baqara banganiba har qarshe Bangani ba...
Wanda a yanda ake ya'da labarin a suratul baqara kawai ake gani....
Na cigaba da budewa Allah cikin ikonsa Na duba suratul Al-imrana, na samu GASHIN ,na duba nisa'i na samu, daga nan WALLAHI kusan ko wace sura na bude sai na samu....
..
..Dahaka ne nadinga dauka daya bayan daya INA taarawa ,wani na iya dauka ,wani Kuma inna dauko sai ya fadi saboda sirantar sa..
SHIN ACIKIN ALQUR'ANI KAWAI AKE GANIN GASHIN KO HAR A WASU LITTAFAN...?
Nayi mamaki da afkuwar hakan ainun....
Sai nayi wani tunani nace bari na duba littafan BOKO... Irinsu Textbooks da Novel da sauran makamantan su.....
Na je na dauko wani tsohon littafi na,Wanda aka rubuta shi,Akan tarihin Samun 'YANCIN NIGERIA ,Na mahaifi NAH na duba Shima na samu ziri daya nagashin Wanda na iya daukowa...sauran sunyi siranta dayawa bazasu dauku ba.....!
SHIN WANNAN GASHIN YAYA KALARSA TAKE..?!
GASHIN zaku sameshi kamar zare ,siriri ,BAQI DA FARI AKWAI KUMA JAA ...
KAMAR YANDA NAGA RUBUTUN WANI DAN UWA YA TABBATARDA CEWAR WANNAN ZAREN ZA'A IYA SAMUNSHI AKOWANE IRIN LITTAFI....DALILIN SAMUWAR SA ,DAGA PUBLISHING COMPANY NE(MA MAIKATAR BUGA LITTAFAI)
SUBHANALLAH..!!!
SHINE WASU 6ARA GURBIN MUSULMI SUKE AMFANI DA WANNAN DAMAR WAJEN KIRKIRAWA ANNABI S.A.W QARYA...
ANNABI S.A.W "YACE DUK WANDA YAYI MINI QARYA DA GANGAR TO YA TATTALI MAZAUNINSA A WUTA...
*BAYAN HAKA GA WULAQANTA LITTAFIN ALLAH.....
Allah kadai yasan adadin mutanen dasuke da janaba ko Haida ko qananun yara marasa tsarki suka dinga daukar ALQUR'ANI..
*AMADADIN A KOMA GA ALLAH AMMA SAI AKE QOQARIN JANYO MANA WATA MASIFAR...
Wal'iyazuBilLAH....
ALLAH YAMANA TSARI DAGA 'YAN DANFARAR IMANI...
ALLAH KADAI YASAN ADADIN MUTANEN DA SUKA JIQA ZARE (DASUNAN GASHI) SUKASHA...
MUTANE IDON SU YARUFE SUNA TUNANIN AKWAI WANDA YA ISA YADAUKE MANA WANNAN MUSIBAR TA CORONAVIRUS BAYAGA ALLAH...?
KO KUN MANTA SHEKARU DASUKA SHUDE...
AKACE MANA ANA GANIN DODON BANGO...
ALLAH YAJIQAN WANI MALAMIN AHLUSSUNAH BADAN YA MUTUBA....
Alokacin muna cikin uqubar wani shugaba,MALAMIN YACE " tunda ana ganin shi shi DODON bangon mai yasa baza'a fa'da masa ba yazo ya murqushe mana wannan azzalumim shugaban In gaskiya ne...
HAka wata yarinya a unguwar mu ,taxi ta qoshi yayi barci ta farka wai sai kawai taga DODON BANGO acikin dakinta....
MUTANE NATA tururuwar zuwa gani ....
Alokacin wasu suce sun ganshi bakai at are dashi ajikin BANGO wasu suce sunganshi complete da sanda.... Alokacin idan mutum bai samu ikon ganinsa ba sai ace wai bashida rabo....
Hatta 'YAN jarida saida suka kawo mata ziyara alokacin.....
...BAyan wasu kwanaki Ashe wai TAMBOTSAN samankanta ne keyi mata gizo..da sauran 6attatun mutanenta.....
HAKA AKAYI ASHEKARUN BAYA DASUKA SHU'DE AKAN EBOLA...
Aka dinga YA'DA jita-jitan shan ruwan gishiri da kuma wanka dashi....
MUTANE suka manta Allah acikin ZUKATANSU....
Sanadin shan ruwan gishiri yayi sanadiyyar Mutuwar MUTANE da da-ma wasu kuma sukamkamu da cututtuka....
Da aka tsananta bincike. Ashe wai PASTOR ne yayi MAFARKI......
....WANNAN KARON KUMA SAI AKAZO DA SABON SALON YAUDARA DAKUMA DAMFARAR IMANI.....
Wanda WALLAHI MUTANE dayawa suntafi ahakan..
..★TO BARA KUJI KU MASU SHAN RUWAN GASHI(ZARE) IDAN SANADIN KAMUWA DA WASU CUTUKAN NE YAZO ALLAH YABADA SA'A★
YAYIN DA MUTANE SUKA MANTA ALLAH AZUKATANSU SAI ALLAH YA BARSU DA IYA WARSU...
ALLAH YASA MUTANE SU HANKALTA...!
YAA! UBANGIJIN MU KARKA KA-MAMU DA LAIFINDA WASU WAWAYE DAGA CIKIN MU SUKE AIKATAWA....
#GA_HUJJA_NAN_NAKAWO_MANA_AWANNAN_HOTON...
#KUNSAN_ITA_HUJJA_ #TAKOBIN_AHLUSSUN_NAH
Safeeyyah Suleiman Umar

Sunday, December 29, 2019

BABBAR MAGANA:



BABBAR MAGANA:
Ranar Lahira Allah yana cewa:
(Ya ku wadanda suka yi imani, ku kiyaye dokokin Allah, kowane mai rai ya dubi abin da ya aikata domin gobe (lahira)…) [Al-Hashri, aya ta 18].
1. Mutuwa ba ita ce karshe ba. Mutuwa mafarin wata rayuwa ce mai tsawon gaske, mai ciki da dadi ko wahala, mai kunshe da farin ciki ko bakin ciki. Duk mai kokwanto game da rayuwar lahira mahaukaci ne ba mai hankali ba.
2. Rayuwarmu a nan duniya tana cike da zalunci da ta'addanci da rashin gaskiya da miyagun ayyuka. An mayar da karya ita ce mafita, yaudara kuma ita ce wayo munafurci kuma ya zamawayewa.
3. A rayuwarmu a yau muna ganin ana hukunta marar laifi a kyale masu laifuka, ana kuma wulakanta mai mutunci sannan a karrama fitsararre. Don haka idan har mun yarda da cewa Allah adalin Sarki ne, to babu makawa dole ne mu yi imani da samuwar wata rayuwa bayan wannan ta duniya da muke ciki, watau rayuwa wadda a cikinta ne Allah zai mayar wa kowane mai hakki hakkinsa, ya hukunta duk wani mai laifi gwargwadon laifinsa. Duk wani mai hankali da ya san ya kamata dole ne ya yarda da haka.
4. Yarda da lahira da imani da sakamakon cikinta ne kadai zai hana wa dan'adam zaluntar dan'uwansa, zai kuma kara wa mutumin kirki kwarin gwiwar aikata ayyukan alheri,domin yana da tabbacin cewa zai ga kyakkyawan sakamakon aikinsa.
5. Ashe bai kyautu mu ci gaba da tunatar da junanmu wannan babbar magana ba

FALALAR RAKA'ATAYIL FAJRI



FALALAR RAKA'ATAYIL FAJRI
*******************************
Raka'atayil Fajri : Sune raka'o'in nan guda biyu na nafila wadanda ake yi bayan Hudowar Alfijir, kafin sallar Asubahi.
Wannan sallar tana da inganci sosai. Domin Annabi (saww) ya bata muhimmanci. Ya kasance yana yinta aduk halin da yake ciki. Koda awajen tafiya, ko azaman gida.
Malamai sun ce ana karanta Fatiha ne da Qul Ya ayyuhal Kafirun, da kuma fatiha da Qul Huwal-Lahu acikinta. KUMA ana yinta ne aboye. (wato yana yin karatunta a sirrance).
Daga cikin falalarta, Sayyiduna Abdullahi bn Umar (rta) ya ruwaito cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) cewa :
"Ya Rasulallahi ina so ka nuna min wani aiki wanda Allah zai amfanar Dani saboda shi".
Sai Annabi (saww) yace masa "KA KULA DA RAKA'ATAYIL FAJRI DOMIN ACIKINTA AKWAI FIFIKO (WATO FALALA)".
(Tabaraniy ne ya ruwaitoshi).
Acikin wata ruwayar kuma Abdullahi bn Umar (ra) yace "Naji Manzon Allah (saww) yana cewa :
"KAR KU BAR YIN RAKA'O'IN NAN GUDA BIYU WADANDA AKEYI KAFIN SALLAR ASUBA. DOMIN ACIKINSU AKWAI ABABEN KWADAYI".
Domin cikar fa'idah ma, ga wani Sahihin hadisin wanda Imamu Muslim ya ruwaito daga Nana A'ishah (ra) ita kuma daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"RAKA'O'I BIYUN ALFIJIR, SUN FI DUNIYA DA ABIN CIKINTA".
Don haka 'yan uwa bai kamata mu rika barin wannan garabasar tana wucemu ba.
Da yawan Matasa Wasu basu yinta. Dama basu kwanciya da wuri, shi yasa suke makara. Kuma da zarar sun tashi sai su sallaci Asubah, ita kuma su kyaleka.
To lallai rashin yin RAKA'ATAYIL FAJRI ba Qaramar Asara bace agareka ya kai Musulmi!
Wannan asarar tafi asarar Biliyoyin Nairori. Domin kuwa Annabi (saww) yace TAFI DUNIYA DA ABIN CIKINTA. Don haka idan baka yita ba, kamar kayi asarar dukiyar dake cikin duniyar nan ne. Ko kuma fiye da haka.
Na san yanzu wani zai ce "Shin zan iya yinta koda bayan Sallar Asubah ne?".
AMSA : A'a. Ana yinta ne kafin sallar Asubah. Domin bai halatta kayi sallar nafila bayan kayi ta Asubahi ba. Har sai bayan fitowar rana.
Hujjah anan ita ce Sahihin hadisin da Imamul Bukhariy da Muslim suka ruwaito daga Abu Sa'eed Alkhudriy (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"BABU SALLAH (NAFILAH) BAYAN SALLAR LA'ASAR HAR SAI RANA TA FADI. KUMA BABU SALLAH BAYAN SALLAR ASUBAH HAR SAI RANA TA BULLO".
Wani Sahabi mai suna Amru bn Abisata (ra) yace "Ya Rasulallahi bani labari mana game da sallah".
Sai yace masa "KA SALLACI ASUBAH SANNAN KA JANYE DAGA YIN SALLAH HAR SAI RANA TA FITO TAYI SAMA.....".
Imamu Ahmad da Muslim ne suka ruwaitoshi).
Mafiya yawan Jamhurin Malamai suna ganin halaccin yin ramukon sallah akowanne lokaci, koda bayan Sallar Asubah din ne. Amma banda nafila.
Saboda hadisin da Imamul Bukhariy da Muslim suka ruwaito daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"DUK WANDA YA MANTA DA WATA SALLAH (TA FARILLAH KENAN) TO YA SALLACETA IDAN YA TUNA".
Amma yin nafila bayan Sallar Asubah, mafiya yawan Sahabbai duk sun karhanta yin haka. Kamar Irin su Sayyiduna Aliyu Bn Abi Talib. Da Ibnu Mas'ud da Zaidu bn Thabit da Abu Hurairah da Ibnu Umara (Allah shi yarda dasu baki dayansu).
Sayyiduna Umar kuwa, ya kasance yakan bugi mutum idan ya ganshi yana yin nafila a irin wadannan lokutan.
Hakanan Sayyiduna Khalid bn Waleed (ra) Shima yakan bugi masu yin hakan. (Wato masu yin nafila alokutan da aka hana).
Duk da cewa akwai Maluman da suka halatta yinta bayan an sallaci Asubah, wai saboda Hadisin wani mutum wanda ya tashi bayan Sallar Asubah yana yinta amma Annabi (saww) bai ce masa komai ba. To amma gaskiya hujjarsu bata kai wannan din Qarfi ba. ta kowacce fuska.
Saboda wannan haka Annabi (saww) yake yi, Haka Khalifofinsa gaba daya suke yi. Hakanan duk manyan Sahabbansa wadanda aka riko sunnah daga garesu duk suna yinta ne kafin sallar Asubahi (Ba bayanta ba) Haka kuma, dukkan Maluman Mazahib din nan guda hudu.
Anan zan tsaya, sai wani lokacin kuma in sha Allahu. Da fatan Allah shi amfanemu da abinda muka karanta.
An gabatar da karatun a Zauren Fiqhu -3 (28-02-2016).
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP. (07064213990).

DALILAI 11 DAKE JAWO ARZIKI



DALILAI 11 DAKE JAWO ARZIKI. DAGA KUR'ANI DA HADIS.
1 Ilimi da kwazon aiki da shi.
2 Dogoro ga Allah ta'ala kawai. suratul dalaki 3
3 Istigifari suratul nuh. 10-12 4 Tuba na gaskiya suratul hud 3
5 Tsoton Allah S.W.T. suratul.A'Araf 96
6 Anbaton Allah a Zuci da baki da gabbai. suratul daha 124
7 Ciyarwa da taimakon na kasa. suratul saba'I. 39
8 Sada zumunta. Buhari, Muslum, Nasaiy, Ibn Majah, Al Imam Ahmad da Abu Dauda
9 Addu'a , Allah ina neman tsarinka daga talauci da kafirci.
10 Taimakawa daliban Ilimi. Attirmiziy
11 Godiya ga Allah ta'ala. suratul Ibrahim 7

KUSKUREN DA MATA SUKE AFKAWA YAYIN 'DAUKEWAR JININ HAILA


KUSKUREN DA MATA SUKE AFKAWA YAYIN 'DAUKEWAR JININ HAILA*
_______________
Mafi yawan mata idan jinin al'ada ya 'Dauke musu suna jinkirta wanka da niyar ko jinin zai Qara dawowa.
Wasu sukan Qara kwana 'Daya zuwa biyu bayan haila ya 'Dauke.
Wasu kuma idan suka ga alama guda 'Daya na 'Daukewar jinin, sai suce zasu jinkirta wanka domin su jira zuwan sauran alamomin. Misali: Mace taaga bushewar gaba amma bata ga Farin ruwa ba, wanda ake kiransa da larabci (قصة البيضاء), daga nan sai tace bari ta bari sai farin ruwa yazo sannan tayi wanka ta cigaba da sallah da azumi.
Duka Wannan kuskure ne babba
Abinda yake wajibi shine: Da zarar taga jini ya tsaya ko taga alamomin Daukewar Jinin haila, toh wajibi ne tayi wanka nan take ta cigaba da ibadar ta. Qin yin wanka har lokacin sallah ya wuce babban zunubi ne.
Allaah ya tanadi Azaba mai tsanani ga masu wasa da sallah.
Allaah yace:-
" ﻓَﻮَﻳْﻞٌ ﻟِﻠْﻤُﺼَﻠِّﻴﻦَ ‏(4 ‏) ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻫُﻢْ ﻋَﻦْ ﺻَﻠَﺎﺗِﻬِﻢْ ﺳَﺎﻫُﻮﻥَ "
{ﺍﻟﻤﺎﻋﻮﻥ : 5-4 }
Allaah ya qara da cewa:-
" ﻓَﺨَﻠَﻒَ ﻣِﻦْ ﺑَﻌْﺪِﻫِﻢْ ﺧَﻠْﻒٌ ﺃَﺿَﺎﻋُﻮﺍ ﺍﻟﺼَّﻠَﺎﺓَ ﻭَﺍﺗَّﺒَﻌُﻮﺍ ﺍﻟﺸَّﻬَﻮَﺍﺕِ ﻓَﺴَﻮْﻑَ ﻳَﻠْﻘَﻮْﻥَ ﻏَﻴًّﺎ "
{ﻣﺮﻳﻢ : 59 }
...... Da ayoyi masu yawa cikin al-Qur'ani.
daga lokacin da jini ya 'Dauke, ibada ya wajaba ga mace.
idan mace ta jinkirta sallah toh sai ta rama su bayan tayi wanka, sannan tayi istigfarin jinkirin sallah
*_Idan kin karanta kiyi Qoqarin turawa yar uwarki musulma zaki samu lada in shaa Allaah_______

FA'IDODIN DA SUKE CIKIN YIN AURE




FA'IDODIN DA SUKE CIKIN YIN AURE
*************************************
Fa'idodin da suke cikin aure ba zasu
Kididdigu ba. Amma ga wasu ka'dan
daga ciki zamu lissafo kamar haka:
1. Yin aure biyayya ne ga Umurnin
Allah da Manzonsa.
2. Yin aure yana sanya Manzon Allah
(saww) farin ciki aranar lahira. Yace :
"Kuyi aure ku hayayyafa. Domin ni
zanyi ma sauran al'ummomi alfahari
daku aranar Alkiyamah".
3. Ta dalilin aure zaka samu wanda
Zai fito ta jikinka, har ya girma yana
Kalmar Shahada!! "LA ILAHA ILLAL
LAHU MUHAMMADUR RASULALLAHI".
4. Ta dalilin aure ne zaka samu
Zuriyar da zasu yi maka addu'a
bayan rasuwarka. Wannan yana daga
cikin ayyukan da ladansu ba zai
yanke ba har abada.
5. Yin aure ya kan zama dalilin
runtsewar idanun mutum daga kalle
kallen Haramun, sannan ya kare masa
al'aurarsa daga Zina.
6. Ta dalilin aure ne zaka samu
damar taimaka ma 'Yar uwarka
Musulma, ka aureta, ka Kiyayeta
kenan daga Zina.
7. Ta dalilin aure ne zaka samu cikar
addininka, da ninkawar ladanka fiye
da wanda bashu da aure.
8. Ta dalilin aure ne zaka samu ladan
ciyarwa da Matarka, da daukar
nauyinta, da ladan samar mata da
Mazaunin da zata rayu.
9. Ta dalilin aure ne zaka samu
damar Qara yawan Musulman duniya
ta hanyar haihuwar da zaka samu.
10. Ta dalilin aure ne zaka samu
damar Karkatar da himmarka daga
kan neman biyan bukatarka ta hanyar
haram izuwa ga hanyar halal. Da
kuma samun ladan saduwa da
iyalanka.
11. Zaka samu lada mai girma sosai
idan Har Allah ya azurtaka da 'Ya'ya
mata guda biyu, kumq kayi hakuri
dasu ka kyautata musu, ka kyautata
tarbiyyarsu, Su zasu zama
Garkuwarka daga shiga wuta.
12. Idan ka har 'Ya'yanka guda biyu
suka rasu, kuma kayi hakuri, to Allah
zai shigar dakai Aljannah saboda
wannan.
13. Ta dalilin aure zaka samu
Qaruwar mutuncinka da darajarka
acikin al'ummah. Ka shiga sahun
mutanen da zasu iya jagorantar
lamuran rayuwar al'ummah.
14. Ta dalilin aure ne zaka Samu
Taimakon Allah cikin al'amarinka.
Kamar yadda Manzon Allah (saww)
yake cewa: "
MUTUM UKU, HAKKI NE
AKAN ALLAH YA TAIMAKESU. 1.
WANDA ZAI YU AURE DON NUFIN
KAME MUTUNCINSA. 2. BAWA
WANDA YAKE NEMAN 'YANCINSA
SABODA YA SAMU DAIDAITUWA
(ACIKIN ADDINI) 3. MUJAHIDI (MAI
YAKIN DAUKAKA ADDININ ALLAH