Tuesday, November 10, 2020

ADDUA GA YARAN MU

 


ADDUA GA YARAN MU
(1) Allah kayi min albarka a cikin 'ya'yana
(2) Allah kayi masu muwafaka su zamo masu yi maka biyayya
(3) Allah ka azurtani da suyi min biyayya
(4)Ya Allah yadda ka sanar da Annabi Musa ilimi ka sanar da 'ya'yana ilimi.
(5) Ya Allah yadda Ka fahimtar da Annabi Sulaiman Ka fahimtar da 'ya'yana.
(6) Ya wanda Ya ba Annabi lukman hikima. Allah ka Bawa Yaya na hikima kuma ka basu iya zance.
(7) Allah Ka bawa 'ya'yana ilimin da basu sani ba.
(8)Allah Ka tunatar da su abinda duk suka manta
(9) Allah ka budewa 'ya'yana albarkar sammai da kasa
(10) Allah Kai mai ji ne kuma mai amsawa ne.
(11) Allah ina rokonka, ka bawa 'ya'yana gam da katar .
(12) Ya Allah Ka basu karfin hadda, kuma Ka basu saurin ganewa,Ka basu kaifin tunani
(13) Allah kasa 'ya'ya na su zamo shiryayyayu, masu shiryarwa
(15) Allah Kai mai ji ne kuma mai amsawa
(16) Allah kar Ka sauyar da Imani a cikin zukatan su.
(17) Allah Ka kawata zukatansu da Imani, Ka sa masu kyamar kafircine
(18) Allah Ka sa masu kyamar fasikanci da kyamar sabon Ka ne
(19) Allah Ka sanya su cikin shiryayyayu.
(20) Allah ka gyara halayen 'ya'yana, Ka cika zukatan su da haske da hikima.
(21) Allah ka tsarkake zukatan 'ya'ya na ga barin riya.
(22) Allah Ka tsare mani gaban 'ya'yana, Ka kare su ga yin zina,Ka kare su daga yin luwadi,Ka kare su daga yin madigo ka kare su da dukkan
laifuffuka ka kare mani zuri'a ta.
(23) Allah Ka sanya 'ya'yana su zamo mahaddatan Al-Qur'ani,su zamo masana Sunnar Annabin Ka(SAW)
(24) Allah Ka azurta 'ya'yana da kamewa da yarda da hukuncin da kayi akan su
(25) Ya Allah Ka azurta 'ya'yana da kaunar Ka da kaunar Annabin Ka da kaunar duk wanda Kake kauna da kaunar duk wani aiki da zai kusantar dasu zuwa ga samun soyayyar Ka.
(26) Ya Allah Ka budewa 'ya'yana kofar arziki na halal daga mayalwaciyar falalar Ka kuma Ka wadatar da su da halal da barin haram.
(27) Allah ka nisantar dasu daga abokai ko kawaye munana da zasu bata tarbiyyar su ko halayen su Ka raba su da alfasha da dukkan mummunan abu.
(28) Allah kasa 'ya'yana su zama masu lafiya a jikin su, Ka kare masu kunnuwan su,Ka kare masu idanuwan su,Ka kare masu rayukan su,Ka kare masu gabbansu ga barin sabon ka ya mai jin kan masu jin kai .Amin Ya Rabbil Alamin.
DON ALLAH WANDA DUK YA SAMI WANNAN ADDUA TO YA TURAWA DAN UWA KO MU RIKA YIWA YARAN MU su zamo nagari.KUMA YA ZAMO SADAQATUL
JARIYA A GAREMU.ALLAH YA SHIRYA MANA SU KUMA YA ALBARKACI RAYUWAR SU AMIN

 

AKWAI DARASI A WANNAN LABARIN!!

 


AKWAI DARASI A WANNAN LABARIN!!
Akwai wani mahaukaci yana bara duk
abinda ka bashi sadaka sai yace
"kayuwa kanka°ranar wata kasuwa ya
shiga kasuwar domin bara,Ashe
akwai wata Mata tanajin haushin
wannan Kalmar da yake fada" wata
Rana ya dawo bara cikin
kasuwar,matar nan ta kirashi ta bashi
sadakar abinci Ashe ta saka guba
(poison) yana karba yace"kinyiwa
kanki• ya juya yayi tafiyarsa,kawai
Mata ta kwashe da dariya tace daka
yau bazaka sake cewa wani yayiwa
kansa ba
...yaje inda yake zama domin cin
abinda ya samo daka bara.kawai
saiga wasu yara sun taso daka
makaranta..sukace da
mahaukaci..kayiwa kanka yau meka
samo ne ka bamu bamu,yace ba
komai sai wani abinci gashi kuci.
suka karba suna murna yace dasu
idan kun gama Ku Kai kwanan cikin
kasuwa..aikuwa suna gamawa daya
Daga cikinsu yace wannan kwanan
kamar Na mamanmu,sukace ehh
shine°ai kuwa suka nufi kasuwa uwar
Na ganinsu da kwano tace a Ina kuka
samu kwano,sukace Kinyiwa kanki ne
ya bamu abinci mukaci
kawai uwar ta Fara kuka
Lallai nayiwa kaina°°'yan uwar mu
tuna duk abinda za muyi mai kyau da
Mara kyau kanmu mukeyiwa...domin
haka idan ka turawa ma wani wannan
sako kaima kayiwa kanka,nidai Na
tura muku Na yiwakaina.
Allah bamu ikon yiwa kanmu alheri.

 

MAI WA'AZI

 


MAI WA'AZI 
so tari in da zai tsaya ya kalli kansa ya duba ayyukansa,kansa ya kamata ya fara yiwa wa'azi kafin waninsa. Domin a Ɗabi'ah mai wa'azi wani lokaci ya kan manta da kansa,in ba wanda Allah yakiyaye shi ba.
Allah nake Roko Ya Ƙara Tabbatar da zuciyoyin mu akan Imani.🤲

IYA ZAMA DA MIJI


 

IYA ZAMA DA MIJI DAGA BAKIN MARIGAYI SHEIKH JA'AFAR (R).
.....................................✍🏼
1- Aurenki ya zama domin neman yardar ALLAh kikayi ba dan tara abin duniya ba.
2- Kada ki zama mai kwadayi wajen zaben mijin Aure.
3- Ki zabawa 'ya 'yanki uba ta hanyar Auren wanda ki ka yarda da addininsa da dabi'unsa harma da dangantakarsa.
4- Ki zama mai riko da addini a gidan mijinki.
5- kada ki zama mai kauracewa shimfidar mijinki.
6- Ki zama mai hakuri da halayyar mijinki.
7- Ki zama mai matukar biyayya ga mijinki.
8- Ki zama kwararriya wajen iya kwalliya kala-kala.
9- Ki zama kwararriya wajen iya girki kala-kala.
10- Ki zama kin iya barkwancin magana wajen baiwa mijinki dariya.
11- Kada ki zama mai rainuwa a cikin duk abinda mijinki ya baki.
12- Ki dinga wanke bakinki da safe da yamma da kuma lokacin kwanciya barci.
13- ki zama mai tsaftar jikinki, gidanki, abincinki, da sauransu.
14- Ki dinga girmama Iyayan mijinki da 'yan uwansa da abokansa.
15- Kada ki zama mai satar kayan mijinki.
16- Kada ki zama mai satar fita unguwa.
17- Ki guji Leke a gidan mijinki, dan yana daga cikin abinda yake raba Aure a tsakanin Hausawa.
18- Ki dinga godewa mijinki a cikin abinda ya baki.
19- ki kiyaye abinda mijinki ya fi so.
20- ki kiyaye abinda mijinki ya fi sonci da safe, rana, dakuma dare.
21- Ki dinga yabawa mijinki kwalliyarsa.
22- Ki dinga yawan neman shawarar mijinki akan duk wani al'amari da zaki yi.
23- Kiyi kwalliya ki tsane tsaf kafin dawowar mijinki.
24- Ki dinga sanya turaren wuta a dakinki, kuma ki kasance mai sanya turare a jikinki a duk lokacin kwanciya.
25- Lallai ki yi kokarin gama aikace-aikacenki kafin dawowar mijinki.
26- Kada ki bari mijinki ya dawo ya sameki gaja-gaja, ki sani kazanta tana haifar da kiyayya.
27- Ki zama mai yawan canza zanen kunshin kafarki da kuma zanen kitso.
28- Kada ki ce mijinki sai ya saya miki abinda ba shida ikon saye.
29- Lallai ki yi amfani da ilimi wajen yanke dukkan wani hukunci.
30- Ki yi shiru a duk lokacin da mijinki yake yi miki fada ko Nasiha.
31- Kada ki zama Al-mubazzara mara tattali.
32- Kada ki tara kayan wanki da yawa a daki, naki ko na mijinki suna wari.
33- Ki tanadi kayan kwalliyar gida bayan na zuwa unguwa.
34- Ki kula da yanayin da zai nuna miki cewa mijinki yana cikin Nishadi ko Damuwa.
35- Kada ki ringa baiwa kawayanki labarin sirrin dake tsakaninki da mijinki.
36- Idan zaki yiwa mijinki magana kiyi masa da tattaunsan harshe, da murya mai karya zukata.
37- Ki zama kin iya kallo mai nuna alamun sha'awa ko soyayya.
38- Idan kika samu sabani da mijinki ki bashi hakuri ko da kuwa kece da gaskiya.
39- Ki zama mai tattali a cikin dukkan abinda kika mallaka a gidan mijinki.
40- Kada ki zama mai kwauron baiwa dangin mijinki abinda ya umarceki da a basu.
41- Kada ki zama mai yin dare wajan girki.
42- Kada ki zama uwar adashi ba tare da sanin mijinki ba.
43- kada ki zama mai yawan fada da makwabtanki.
44- Kada ki kasance mai yawan zagi ko Ashariya.
45- Kada ki ringa baiwa Iyayanki Labarin laifin da mijinki yake miki.
46- Ki zama mai hakuri da juriya da halayyar Iyayan mijinki da 'yan uwansa.
47- Idan mijinki ya yi miki laifi kada ki nuna masa bacin ranki a gaban iyayanki ko 'yan uwansa.
48- Kada ki ringa daga murya sama idan kuna sa-in-sa da mijinki.
49- Kada ki rinqa baiwa 'yan uwan mijinki labarin laifukansa.
50- Ki dinga yiwa mahafiyar mijinki Ihsani da 'yanuwansa.
51- kidinga yiwa mijinki addua tamusamman kamar lokacin walha ko bayan yafita zuwa wajen nemo abinda zakuci kuyi sutura.
52- kizama mai son ibada, nesa nesa da qawaye da son zuwa neman ilimi na Addininki don Sanin yadda zaki bautawa Ubangijinki dasauransu, kuma ki nemi ilimin zamani don sanin yadda zaki zaman duniya cikin rufin asiri da sanin yakamata.
*Ga Amana nan mun baki/ka katurawa mata ko maza domin a Isar zuwa ga 'yan uwa mata kuma uwayenmu don ceto su damu gaba daya daga kaidi da tarkon shitan la'ananne.*
*Mugudu tare mutsira tare*👏