TARBIYYAR YARA A MUSULUNCI. //1
TARBIYYA hakkine da Allah (SWT) ya wajabtawa Iyaye suyi ga 'ya'yansu, kamar yadda ya wajabtawa 'ya'ya yin biyayya ga iyayensu.
Kamar yadda muka sani, 'ya'ya kyautace (Ni'imace) daga Allah da yake bayar da ita ga wanda yaga dama, kuma Amanace da Allah ya dankata a hannun iyaye. Sabida haka Iyayen da suka kyautata wajen tarbiyyantar 'ya'yansu da ladabtar dasu bisa koyarwar Musulunci, to sun sauke wannan amanar, Wadanda kuma suka yi sakaci kuma suka takaita wajen yi musu tarbiyya to sun tozarta wannan Amanar.
Allah Ta'ala yace: " Ya ku wadanda su kayi imani, ku tsare kawunanku da iyalanku daga wuta, wacce mutane da duwatsu ne makamashinta... "
(Tahrim: 6).
Annabi (SAW) yana cewa a wani hadisi:
" Dukkanninku masu kiwone kuma ababan tambayane dangane da kiwon da aka baku, shugaba me kiwone (dangane ga talakawansa) kuma abin tambayane dangane da kiwon da aka bashi, mutum me kiwone dangane ga iyalinsa kuma abin tambayane dangane da kiwon da aka bashi."
Bukhari da Muslim.
Akwai wasu hanyoyi wadanda idan muka bisu zasu taimaka mana da yardar Allah wajen Tarbiyyar 'yayanmu, daga cikinsu akwai:
1. MU ZABAWA 'YA'YANMU UWA TA GARI.
Auren mace tagari muhimmin lamarine dake taimakawa wajen tarbiyyar 'ya'ya, domin uwa ita ce makaranta ta farko da yaro ke daukar darasi a cikinta, kuma halaye da dabi'un uwa suna tasiri matuka ga 'ya'yanta, sabida hakane shari'a ta kwadaitar damu wajen auren mace tagari ma'abociyar addini.
Annabi (SAW) yana cewa: " Ana auren mace sabida abubuwa guda 4; dukiyarta, da kyawunta, da daukakarta, da addininta. ka zabi ma'abociyar addini, sai hannunka yayi albarka."
Bukhari da Muslim.
Abu ne mai muhimmanci ga wanda yake da niyyar yin aure ya dage da addu'a akan Allah ya azurtashi da samun mace tagari, kuma yayi "istikhara" wato neman shawarar (zabin) Allah kafin auren, ya kuma nemi shawarar bayin Allah mutanen kirki, sannan yayi kokari wajen yin bincike akan nagartar yarinyar da kuma iyayenta, ya kuma fawwala al'amuransa zuwa ga Allah SWT.
Sannan kuma ya zama wajibi abi hanyoyin da Shari'a ta tsara wajen neman aure, kuma a nisanci sabawa Allah da sunan murna ko farinciki a yayin aure, wannan zai sa Allah Ta'ala ya sanya Albarka a cikin auren da kuma zuriyar da za a samu ta dalilin wannan auren.
2. ROKON ALLAH YA BAKA ZURRIYYA TA GARI.
Wannan dabi'ace ta Annabawa da Manzanni da bayin Allah salihai. Kamar yadda Allah ya bamu labari a kissar Annabi Zakariyya (AS), yake cewa: " A yayin nan Annabi Zakariyya ya roki Ubangijinsa, yace: ya Ubangiji ka bani kyauta daga gareka ta zuriyya tsarkakakkiya, hakika kai mai amsar addu'ane."
(Ali-Imran: 38)
A wata ayar kuma Allah ya bamu labarin salihan bayinsa, daga cikin siffofinsu suna addu'ar Allah ya basu mata da 'ya'ya nagari, yake cewa:
" Wadannan da suke cewa ya Ubangijinmu ka bamu kyauta daga matayenmu da zuriyyarmu abinda idanuwanmu za suyi sanyi dasu, kuma ka sanyamu mu zama shugabanni ga masu tsoron Allah."
(Al-furqan: 74)
Wannan ya nuna mana muhimmancin addu'a da rokon Allah wajen samun 'ya'ya nagari kasancewar har Annabawan Allah da Salihai sun yi irin wannan addu'ar.
Allah ya bamu ikon yiwa 'ya'yayenmu tarbiyya da ladabdar dasu bisa koyarwar Kur'ani da Sunnah,
TARBIYYA hakkine da Allah (SWT) ya wajabtawa Iyaye suyi ga 'ya'yansu, kamar yadda ya wajabtawa 'ya'ya yin biyayya ga iyayensu.
Kamar yadda muka sani, 'ya'ya kyautace (Ni'imace) daga Allah da yake bayar da ita ga wanda yaga dama, kuma Amanace da Allah ya dankata a hannun iyaye. Sabida haka Iyayen da suka kyautata wajen tarbiyyantar 'ya'yansu da ladabtar dasu bisa koyarwar Musulunci, to sun sauke wannan amanar, Wadanda kuma suka yi sakaci kuma suka takaita wajen yi musu tarbiyya to sun tozarta wannan Amanar.
Allah Ta'ala yace: " Ya ku wadanda su kayi imani, ku tsare kawunanku da iyalanku daga wuta, wacce mutane da duwatsu ne makamashinta...